RASHIN TSARO: Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida, ɗan sanda ɗaya da wasu mutane 13 a cikin mako daya a Najeriya

Akalla mutum 20 ne ‘yan bindiga suka kashe daga ranakun 26 ga Disambar 2021 zuwa 1 ga Janairu 2022.

Bisa ga ƙididdigar da aka yi an samu raguwar akalla kashi 80 cikin 100 akan waɗanda aka kashe a makon jiya a kasar.

Daga ckin mutum 20 din da aka kashe a makon da ya gabata akwai sojoji shida, dan sanda daya sannan da Wani basarake.

PREMIUM TIMES ta tattaro adadin yawan mutanen da aka kashe daga rahotannin da jaridu suka wallafa kamar haka.

Jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutum 16 sannan sun yi garkuwa da mutane da dama a wasu kauyukan jihar.

A ranar Lahadin da ya gabata ‘yan bindiga sun kashe mutum 7 sannan suka yi garkuwa da mata 33 a kauyuka bakwai dake karamar hukumar Gusau.

Wadannan kauyuka sun hada da Geba, Kura, Duma, Gana, Tsakuwa, Gidan Kada da Gidan Kaura.

Da dama dake zama a karamar hukumar sun nemi mafaka a Damba Estate dake cikin garin Gusau.

Bayan haka ‘yan bindigan sun kai farmaki kauyen Gada dake karamar hukumar Bangudu inda suka kashe wani sarki a gundumar mai suna Umaru Bawan-Allah da wasu mutum biyar ranar Laraba.

Sakataren masarautar Bangudu Usman Ahmad ya bayyana cewa maharan sun far wa kauyen da misalin karfe daya na dare ne

Jihar Osun

A ranar Litinin makon jiya mahara suna kashe mutum daya a taron karshen shekara da ake yi a kauyen Igbaye jihar Osun.

Wani jami’in tsaro wanda baya so a fadi sunansa saboda tsaro ya ce an kashe mutumin ne a dalilin rashin jituwan da aka samu a tsakanin wasu mutane a wurin taron.

Jami’in tsaron ya ce mutumin ya rasu a lokacin da likitoci ke duba shi a asibiti.

Jihar Barno

Sojoji 6 ne ‘yan bindiga suka kashe a ranar Alhamis a lokacin da dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa suka fatattaki ‘yan ta’addan Boko Haram da ƴan kungiyar ISWAP a kauyen Mallam Fatori da ke kusa da tafkin Chadi.

Wani jami’in tsaro ya ce dakarun sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 22 a arangamar da aka yi.

Jihar Anambra

‘Yan bindiga sun kashe ɗan sanda ɗaya a kauyen Ihiala dake jihar Anambra

Ɗan sandan ya gamu da ajalinsu ne a lokacin aikin sa wajen yin rakiyar wasu jami’an asibitin dake aiki a kauyen ranar Larabar da ya gabata.

Jihar Delta

Mutum uku ne suka rasa rayukansu a wani harin da ‘yan bindiga suka kai a tashar motoci dake jihar Delta ranar Alhamis din makon jiya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bright Edafe Wanda ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a ya ce rundunar ta yi batakashi da wasu ‘yan fashi da makami da suka kawo hari tashar motoci dake karamar hukumar Udu.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

A ziyarar da ya Kai jihar Barno ranar 24 ga Disambar 2021 shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin kawo karshen rashin tsaro ka iya hana a samu ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa.