QATAR 2022: Shugaban FIFA ya ragargaji ƙasashen Turai, ya kira su ‘munafukan banza, munafukan wofi’

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, Infantino, ya ragargaji ƙasashen Turawan Yamma masu sukar Qatar kan zargin take ‘yancin ɗan Adam.
Infantino ya kira su munafukan banza, munafukan wofi, a wata tattaunawa da ya yi da taron manema labarai a Doha, babban birnin Qatar, ranar Asabar, jajibirin fara fafata gasar.
Kakkausar maganar Infantino ta zo ne dangane da caccakar Qatar da ake yi cewa baƙi ‘yan ƙasashen waje da su ka je aikin ƙarfi Qatar wajen gina filayen wasa sun mutu da dama, har mutum 6,500.
Infantino ya ce ya kamata a dubi irin ƙoƙarin da Qatar ta yi wajen shirya gagarimin taron gasar.
Ya ce, “idan ana maganar take haƙƙin ɗan Adam, ai babu wanda ya kai ƙasashen Turawa.
“Haƙƙin da Turawa su ka danne a duniya shekaru 3,000 baya, ya yi munin da sai sun shekara 3,000 nan gaba su na neman afuwa kafin a saurare su.
“Ni Baturen asalin Italiya ne, haifaffen Sweden. Idan kun yi maganar take haƙƙin ma’aikata baƙi a Qatar, ai baƙi masu son shiga ƙasashen Turai neman aiki har mutum 25,000 suka mutu, saboda an rufe kan iyakoki, an hana su shiga tsakanin 2014 zuwa 2022..
“Dubban baƙi sun shiga Qatar ta hanyar da doka ta gindaya, sun yi aiki, sun samu kuɗi nunki 10 na abin da za su samu a ƙasashen su ko wasu ƙasashen Turai.
“Kuma ai kamfanonin ƙasshen Turai ne su ka yi aikin gine-gine a Qatar, kuma a wurin su baƙin da ake cewa ana danne masu haƙƙi su ka yi aiki a Qatar.”
Infantino ya ce “ina jin kai na ni Bature ne, ina jin kai na ni Balarabe ne, ina jin kai na ni baƙin ma’aikatan Qatar ne. Ina jin kaina ni mace ce. Duk wanda ya danne min haƙƙi ba zan ji daɗi ba. To amma ni tun ina a ƙaramin yaro aka fara nuna min wariyar launi a Turai, saboda ina da jan gashi sosai a kai na.”
Ya ce FIFA ta yi rawar gani a Qatar wajen sa gwamnatin Qatar yanka wa ma’aikata ƙa’idar mafi ƙanƙantar albashi, ‘yancin damar sauya wurin aiki da sauran haƙƙoƙi.
Ko a ranar Juma’a sai da FIFA ta amince da dokar Qatar ta haramta shan giya da sayar da ita a filayen ƙwallon ƙasar guda 8 da za a yi wasannin cikin kofin duniya, wanda za a fara a ranar Lahadi.