QATAR 2022: Ƴan Wasan Da Su Ka Fi Yawan Shekaru Da Waɗanda Su Ka Fi Saura Zuwa Gasar Kofin Duniya

Mai tsaron gidan ƙasar Mexico, Alfredo Talavera ya fi dukkan ‘yan wasa 831 da su ka halarci gasar lashe Kofin Duniya na Qatar 2022, wanda za a fara fafatawa a ranar Lahadi.

Shekarun Talavera 40, wato ya fi ɗan wasan Portugal Pepe da Thiago Silver na Brazil yawan shekaru, saboda kowanen su shekarar sa 38.

Ɗan wasa Atiba Hutchinson na Canada ne na biyu a yawan shekaru, mai shekara 39, shi da Eji Kashima na Japan da Remko Pasveer na Netherland.

Masu shekaru 38 sun haɗa da Pepe, Thiago Silver da Aymeen Mathlouki na Tunisiya.

Cristiano Ronaldo, Luca Modric na Croatia, Bryan Ruiz Costa Rica su ne ‘yan shekaru 37.

Cristiano Ronaldo da mai tsaron gidan Amurka Guillerno Ochoa sun fi sauran yawan zuwa gasar kofin duniya. Kowanen su Qatar 2022 ne zuwan sa ba biyar.