PDP ta nemi Buhari ya shirya taron gangami kan matsalar tsaro

Jam’iyyar PDP ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta kiran taron gangami na kasa kan matsalar tsaro, yadda jama’a da dama za su iya bayar da gudummawar shawarwarin yadda za a shawo kan matsalolin.
“A taron Kwamitin Zartaswa na PDP da mu ka gudanar a ranar Alhamis a Abuja, wannan jam’iyya na cike da damuwar yadda matsalar tsaro ke neman gagarar wannan gwamnati.
“PDP na bai wa Buhari shawara ya kira taron gangami na kasa baki daya, domin a ji ra’ayoyin mutane da dama, kan yadda za a magance wannan gagarimar matsala.”
Har ila yau PDP na ba Buhari shawara ya kafa dokar ta-baci kan matsalar tsaro a kasar nan.
Idan ba a manta ba, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, kuma jigo a PDP, Bukola Saraki, ya shawarci Buhari cewa ya gaggauta neman taimakon yadda za a magance matsalar tsaro, domin lamarin fa ya fi karfin sa.
Haka shi ma Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya nemi Buhari ya shirya taro kan matsalar tsaro a kasar nan.
Shi ma Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Filato, Honorabul Bangos, ya ce Majalisar Tarayya ta shirya taro kan matsalar tsaro a ranakun 24 da 28 Ga Mayu. Ya kara da cewa bayan taron, ba za su sake bai wa Buhari uziri ba, idan ya kasa tabuka komai, to za su ba shi zabin ya sauka daga mulki a cikin aminci da mutunci, ko kuma su tsige shi.
Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, wanda shi ma jihar sa ta fada cikin tashe-tashen hankulan da ta kai shi ga kakaba dokar hana walwala a wasu yankuna, ya hakkake cewa rikice-rikicen da ke faruwa a kasar nan na da nasaba da siyasa.