NDLEA ta kama Ƴan kwaya 1,232 a shekarar 2022 a Kaduna

Hukumar Hana Sha da Fataucin muggan kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana cewa ta kama ƴan kwaya mutum 1,232 da haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogram 15,104.555 a jihar Kaduna.
Kwamandan hukumar na jihar Kaduna Ibrahim Baraje ya sanar da haka a garin Kaduna rana Alhamis inda ya ce hukumar ta yi wannan kame daga watan Janairu zuwa Disambar 2022.
Baraje ya ce daga cikin mutum 1,232 din da aka kama akwai mata 64, maza kuma 1,163.
Ya Kuma ƙara da cewa daga cikin kilogram 15,104.555 na haramtattun kwayoyin da aka kama akwai ganyen wiwi mai nauyin kilogram 7, 432.942, madarar hodar ibilis mai nauyin kilogram 7, 432.942, hodar ibilis kilogram 1.487, Methamphetamine kilogram 0.767, Tramadol kilogram 1, 880.102 da wasu haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogram 5, 789.008.
Baraje ya ce a tsakanin wannan lokaci kotu ta yanke wa ‘yan kwaya mutum 199 hukunci, mutum 350 na jira a yanye musu hukunci sannan hukumar ta kula da mutum 683 dake fama jirkicewar kwakwalwa a dalilin kwayoyin da suke sha.
NDLEA ta kama wurare 132 da ake siyar da kwayoyi sannan sun lalata kayan masu jarƙallar muggan kwayoyi 27.
Ya ce hukumar a shirye take domin yakan sha da fataucin muggan kwayoyi kuma hukumar ba za ta ja da baya ba har sai ta gama da ƴan kwaya a jihar Kaduna.
A karshe Baraje ya yi kira ga mutane da su hada hannu da hukumar domin yakar muggan kwayoyi a jihar kwatakwata.
“Muna kira ga iyaye da su rika sa wa ƴaƴan su ido suna tsawata musu a koda yaushe kada su fada cikin wannan matsala na shaye shayen kwayoyi.