NAJERIYA TA BUƊE WUTA: An yi wa mutum sama da miliyan 1.6 allurar rigakafin Korona a ƙasar

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa gwamnati ta yi wa mutum sama da miliyan 1.6 allurar rigakafin cutar korona a kasar nan.

Shu’aib ya fadi haka ne a taron da kwamitin PSC ta yi da manema labarai ranar Litini a Abuja.

Ya ce zuwa yanzu mutum 1,692,315 sun yi allurar rigakafin korona da ruwan maganin AstraZeneca zango na biyu a kasar nan.

Shu’aib ya ce gabaɗaya yanzu mutum 4,052,756 ne suka yi allurar rigakafin korona a Najeriya.

“Daga ciki, an yi wa mutum 2,645,020 allurar rigakafin cutar da ruwan maganin AstraZeneca ne a zangon farko sannan mutum 1,407,736 sun yi da ruwan maganin Moderna.

“Mutum 1,692,315 ne suka yi allurar rigakafin cutar da ruwan maganin AstraZeneca sannan zuwa yanzu gwamnati ta yi amfani da kashi 70.4% na kwalaben maganin rigakafin korona na Moderna guda 2,000,040.

Allurar rigakafin korona a jihohin kasar nan

Shu’aib ya ce zuwa yanzu jihohin kasar nan sun yi amfani da kashi 50% na kwalaben maganin rigakafin Moderna da suka karba sannan har sun rage saura domin yi wa mutane rigakafi zango na biyu.

Ya ce a dalilin haka jihohi sun dakatar da yi wa mutane allurar rigakafin da ruwan maganin Moderna sun ci gaba da karisa wa wadanda suka yi allurar rigakafin da ruwan AstraZeneca zango na biyu.

Shu’aib ya yi kira ga jihohin da basu sanar da wuraren yin allurar rigakafin a gidajen jaridu da kafafen sada zumunta a yanar gizo.

Ya ce gwamnati za ta hukunta duk jihar da ta kama tana bari mutane na karbar katin shaidar yin allurar rigakafin korona ba tare da sun yi allurar ba ko kuma suna karba kudi wajen mutane kafin a yi musu allurar rigakafin.