KORONA: Gwamnati ta cire kasar India daga jerin kasashen da aka yi wa katanga da Najeriya

Gwamnatin tarayya ta cire kasar India a jerin kasashen da ta hana mutane daga kasar nan zuwa sannan da mutane daga can zuwa Najeriya saboda yaduwar sabuwar samfurin korona dake yi wa mutane kisan faradɗaya, wato nau’in ‘Delta Variants’.

Shugaban kwamitin PSC Boss Mustapha ya sanar da haka a taron da kwamitin ta yi da manema labarai ranar Litini a Abuja.

Mustapha ya ce gwamnati ta cire kasar ne bayan ganin nasarorin da kasar ta samu wajen rage yaduwar cutar.

Yaduwar cutar korona a kasar Inda.

Zuwa yanzu kasar India ta yi nasarar rage yaduwar cutar korona a kasar domin a watan da ta gabata mutum ƙasa da 40,000 ne suka kamu da cutar a kasar.

Kasashen da aka yi wa katanga da Najeriya

Idan ba a manta ba ranar 1 ga Mayu ne Kwamitin PSC ya sanar da sabuwar dokar da gwamnati ta kafa cewa duk fasinjan da zai sauka Najeriya daga Indiya ko Brazil ko Turkiyya, tilas ne a killace shi tsawon kwanaki bakwai, kafin a bar shi ya shiga cikin garuruwan Najeriya.

Bijiro da wannan doka ya biyo bayan bullar sabuwar samfurin cutar korona mai yawan kisan mutane birjik musamman a Indiya da Brazil.

Bayan haka a watan Yuni gwamnati ta saka kasar Afrika ta Kudu a jerin kasashen da ta hana mutane daga kasar nan zuwa sannan da mutane daga can sauka a Najeriya.

A lokacin gwamnati ta yanke wannan hukunci ne saboda ftinar da ta hango na kokarin dannowa Najeriya.

Bisa ga dokar gwamnati ta ce duk Dan Najeriya da ya dawo daga wadannan kasashe sai ya killace kansa na tsawon kwanaki 14 kafin a bari ya shiga garuruwan kasar nan.