Najeriya ba ta iya kera makamai saboda dukkan kudaden da ake ware wa sojoji na karewa wajen biyan su albashi – Gbajabiamila

Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya nuna damuwa dangane da rashin wadatattun kudaden da za su wadaci sojoji su kera makamai.

Ya bayyana cewa kashi 91% bisa 100% na kasafin kudaden da ake ware wa fannin tsaro na sojojin Najeriya, duk su na tafiya ne wajen biyan sojoji albashi da biyan su alawus-alawus da kuma ayyukan tafiyar da tsare-tsaren gudanarwa.

Gbajabiamila ya yi wannan karin haske ne yayin da ya ke jawabi wurin zaman sauraren “Kudirin Dokar Kafa Gidauniyar Tallafa Wa Sojoji da Kudade”, wato “Armed Forces Trust Fund”, a ranar Litinin a Abuja.

“Da yawan ku za ku yi mamakin dalilin yunkurin kafa wannan gidauniya da ake yi. To zancen gaskiya kudaden kasafin da ake ware wa sojoji ya yi kadan, domin kashi 91% bisa 100% na kudaden na tafiya wajen biyan albashi, alawus-alawus da kudaden tafiyar da ayyukan yau da kullum. Kashi 9% bisa 100% ne kadai ke raguwa domin a sayi makamai da su.”

Ya kara da cewa a halin yanzu Najeriya na gaganiya da yake-yake ta ko’ina a kasar nan. “Ga Boko Haram, ga ‘yan bindiga, ga masu garkuwa da mutane, ga kuma sauran masu tayar da fitintinu a bangarorin kasar nan. Don haka akwai bukatar karin kudi ga sojoji domin an kai ga fara kera makamai a nan cikin gida.” Inji shi.

Honorabul Babajimi Benson dan APC daga jihar Legas ne ya gabatar da kudirin, kuma dama shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Tarayya kan Harkokin Tsaro.

Kudirin dai ya tsallake siradin karatu na biyu tun cikin watan Fabrairu.

Idan doka ta tabbata, za a rika tatsar kudade daga Asusun Gwamnatin Tarayya, Gidauniyar NSWF, harajin tikitin jiragen sama, cinikin lodin kayayyakin manyan jiragen ruwa da harajin jiragen sama da ake dauka shata ana dankarawa cikin Asusun Gidauniyar Tara Kudaden Sojojin.

Sai dai kuma Gbajabiamila bai yi tsokaci kan zargin karkatar da makudan kudaden sayen makamai da aka rika zargin manyan fararen hula da manyan sojoji sun rika yi, a matsayin inda kudaden sojoji ke tafiya ba.