“Na shuka alkhairin da za ku riƙa tunawa da ni bayan na tafi” Shugaba Buhari

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ƴan Najeriya ba za su fahimci tasirin ayyukan da yake yi ba, sai bayan ya sauƙa daga kan ƙaragar mulki.
Ya fadi hakan ne a lokacin da yake naɗa sabbin shugabannin hukumar kula da asusun zuba jarin ƙasashen waje wato NSIA, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

A wani taƙaitaccen biki da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, Buhari ya buƙaci sabbin shugabannin su mayar da hankali wajen ganin an sake samun kari a zuba hannayen jari da za su taimaka wajen tayar da komaɗar tattalin arziki, yayin da ake hasashen farashin ɗanyen mai zai faɗi zuwa dala 40 kan kowacce ganga kafin shekara ta 2030.

“Na shuka alkhairin da za ku riƙa tunawa da ni bayan na tafi” Shugaba Buhari
Gwamna Tambuwal ya tsaurara matakan tsaro a Sokoto

Shugaban ya jaddada matsayin gwamnatinsa na ƙirƙiro ayyukan dogon-zango da shirye-shirye da za su samar da ayyuka a Najeriya.
Kuma yana mai cewa ba za a fahimci tasirin ayyukan da yake bijiro da su ba a yanzu sai lokacin da ya bar mulki, saboda tsare-tsarensa da ayyukansa na dogon-zango ne.
Buhari ya ce babu shakka wannan sauyin da suke faɗi za su faru amma ba kamar yadda wasu ke tsammani ba wato a lokaci guda.

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaGwamna Tambuwal ya tsaurara matakan tsaro a Sokoto

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce dake da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jaridu.