MUTUWA TA RATSA SARAKUNA: Ta ɗauki ran Olubadan na Ibadan a farkon 2022

Babban Basaraken ƙasar Ibadan, Olubadan Saliu Adetunji ya rasu. PREMIUM TIMES ta samu tabbacin rasuwar basaraken ne daga bakin majiyar da ta roƙi a ɓoye sunan ta.

Majiyar ta ce babban basaraken na Yarabawan ƙasar Badun ya rasu a Babban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan (UCH), da asubahin ranar Lahadi.

Kakakin Yaɗa Labaran Sarki Saliu Adetunji mai suna Yanju Adegboyega ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba shi da iznin yin wata magana ko ƙarin haske dangane da mutuwar basaraken, wanda shi ne Sarki na 41 a Ibadan.

An naɗa shi sarauta a ranar 4 Ga Maris, 2016. Kuma shi ne ɗa na 17 a wurin iyayen sa. An haife shi a ranar 28 Ga Agusta, 1928.