Gwamnatin Kaduna ta rufe makarantun islamiyya biyu saboda zargin yi wa ɗalibai fyade

Idris Aliyu, shugaban hukumar kula da makarantun Jihar Kaduna ya bayyana cewa hukumar sa ta rufe wasu makarantun Islamiyya biyu saboda zargin kama su da laifin yi wa wasu yaran makaranta mata biyu fyade.

Daya daga cikin makarantar Madrasatul Ulumul Deeniya wa Tahfizul Qur’an, dake unguwar Rigasa ana zargin ɗaya daga cikin malamin makaranta da yi wa wata ƴar shekara shida fyaɗe a makarantar.

Aliyu ya kara da cewa an gano cewa wani malami a makarantar ya yi wa yarinyar fyade amma kuma makarantar suka boye abin.

Tun farko kakar ƴarin ta tunkari mahukuntar makarantar domin yi musu kukan abinda aka yi wa jikarta amma maimakon su saurareta sai suka haɗu da wasu daga cikin ɗaliban makarantar suka lakaɗa mata dukan tsiya.

Duk da tabbacin yin lalata da ƙarfin tsiya da likitoci suka tabbatar, shugaban makarantar ya karyata haka.

” Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umarci hukumar ta rufe makarantar har sai an kammala bincike akai.

Makaranta ta biyu kuma shi malamin mai shekaru 50 an kama shi da laifin yi wa ƴar shekara 12 ciki ne a makaranta.

A karshe Aliyu ya bayyawa Kamfanin dillacin Labaran Najeriya cewa kwamishinonin Ilimi da na jin daɗi da walwalan jama, za su yi aiki tare da rundunar ƴan sanada don n tabbatar da an bo wa waɗannan yara hakin su sannan kuma a hukunta waɗanda suka aikata wannan abu.