Mutum hudu sun kamu da cutar ‘Kyandan Biri’ a jihar Ogun

Shugaban fannin kiwon lafiyar mutane na ma’aikatar lafiya na jihar Ogun Festus Soyinka ya bayyana cewa mutum hudu sun kamu da cutar Monkey pox a jihar.

Soyinka wanda ya sanar da haka wa manema labarai a garin Abeokuta ranar Alhamis ya ce an gano wadannan mutane a kananan hukumomin Ado-Odo/Ota, Abeokuta ta Arewa da Abeokuta ta Kudu.

Zuwa yanzu mutum 7 ne suka kamu da cutar a jihar.

Ya ce gwamnati ta dauki tsauraran matakai domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Yaduwar cutar monkey pox a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa daga watan Janairu zuwa 7 ga Agusta 2022 mutum 172 ne suka kamu da cutar monkey pox sannan cutar ta yi ajalin mutum 12 a kasar nan.

NCDC ta tabbatar cewa sama da kashi 50% na mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya maza ne.

An samu mutum 60 da ake zargin sun kamu da cutar Inda sakamakon gwajin cutar ya tabbatar da mutum 15 da suka kamu daga jihohin 9 da Abuja.

Wadannan jihohi sun hada da Ondo -2, Rivers -2, Abia -1, Anambra -1, Ebonyi -1, Edo -1, Ogun -1, Nasarawa -1 da FCT -2.

NCDC ta ce tun bayan bullowar cutar a Satumba 2017 an samu mutum 985 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 35.
Sakamakon gwajin cutar ya tabbatar da mutum 389 da suka kamu da cutar inda a ciki akwai maza 263 da mata 135 daga jihohi 30.

Hukumar ta kuma ce bana cutar ta yi ajalin mutum 12 a jihohi 9.

Wadannan jihohi sun hada da Lagos -3, Edo -2, Imo -1, Cross River -1, Rivers -1, Ondo -1, Delta-1, Akwa Ibom -1 da FCT -2.

NCDC ta tabbatar cewa gwamnati ta dauki matakai da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Yaduwar cutar a duniya

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa cutar ta ci gaba da yaduwa a kasashen duniya inda zuwa yanzu mutum 35,000 suka kamu da cutar a kasashe 92.

WHO ta ce cutar ta yi ajalin mutum 12 a duniya.

Kungiyar ta ce cutar ta fi yaduwa a tsakanin mazan dake saduwa da maza.

Menene cutar Monkey pox

Cutar ‘Monkey Pox’ cuta ce da take kama fatar mutum inda zaka ga mai dauke da cutar na fama da wasu irin manya-manyan kuraje kamar kazuwa.

Cutar ya fara bullowa a Nahiyar Afrika a shekarar 1970 sannan ya bayyana a shekaran 1978 a Najeriya.

Tun daga wancan lokaci cutar bata sake bayyana ba sai a shekarar 2017 a jihar Bayelsa.

Hanyar da cutar Monkey pox ke shiga jikin mutum

Rahotanni sun nuna cewa namun daji kamar su birai da beraye dake shawagi a gidajen mutane na daga cikin ababen dake kawo cutar ‘Monkey Pox’.

Sannan kuma cutar na yaduwa idan ana yawan zama kusa da wadanda suka kamu da cutar.

Ana kuma iya kamuwa da cutar idan aka yi jima’i da wanda ya ke ɗauke da cutar.

Alamun cutar sun hada da Zazzabi, yawan jin gajiya a jiki, ciwon jiki musamman baya, kumburin jiki musamman idan cutar ta fara nunawa, bayyanan kuraje a jiki.

Hanyoyin da za a bi domin guje wa kamuwa da cutar.

1. A daina cin naman dabbobin daji kamar su biri, burgu da bera.

2. A hana dabbobi yawo musamman wadanda ke kiwon su domin kada su fita su dauko cutar daga jikin dabbobin da suke dauke da cutar kuma a killace dabbobin da suka kamu da cutar saboda hana yaduwar ta.

3. Mutane su nisanta kansu daga dabbobi musamman daga kashin su da kuma jikinsu.

4. Kada a zauna daki daya da mutanen da suka kamu da cutar.

5. A yi amfani da safan hannu wajen kula da mutanen da suka kamu da cutar musamman ma’aikatan asibiti sannan idan aka ziyarci wanda ke dauke da cutar a tabbatar an wanke hannaye da ruwa da sabulu bayan an fito.

6. A tabbatar cewa a kowani lokaci ana tsaftace muhalli.

7. Sumbatar mai dauke da cutar kan iya sa a kamu.

8. A rage shan hannu ko ta yaya sannan a yi amfani da man tsaftace hannu.

9. Hukumar dakile yaduwar cututtuka dake kasar Amurka CDC ta ce Kaurace wa juna, mutum zai iya yi wa kansa wasa har sai ya samu gamsuwa da rufe bangaren jikin da kurarrajin cutar suka feso kafin a sadu.