Ina da laƙanin kawo ƙarshen matsalar wutar lantarki a Najeriya – Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban ƙasa na jami’yyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana da laƙanin da zai hanyar kawo karshen matsalar wutan lantarki da ake fama da shi a Najeriya.
Atiku ya ce idan aka zabe shi shugaban ƙasa zai ba jihohin kasar nan damar samar da wutar lantarki a jihohin su.
“Idan kamfanin wutan lantarki na rikici da gwamnatin tarayya a Abuja bai kamata ya shafi wani kamfanin a jihar Legas, ko Kano, ko a Aba ba ko Kuma ya shafi talakan Najeriya dake da bukatan kallon labarai da yin barci da fanka ba.
“Tsari na farko a hanyar kawar da matsalar wutar lantarki shine a baiwa ƴan kasuwa su saka jari.
” Kirkiro da sabbin hanyoyi da za su rika samar da wutar lantarki ba lallai ta hanyar da ake samarwa yanzu ba. Za a samu ta hanyar hasken rana da iska da sauran hanyoyi na zamani.
Atiku ya kara da cewa zai yi amfani da kwarewarsa a fannin kasuwanci da saka jari domin tabbatar da ganin madu hannu da shuni sun shigo harkar samar da wutar lantarki domin ya wadata a kasar nan.
Bayan haka ya jawo hankalin masu saka jari da garzayo su saka jari a harkar a kasar nan domin cigaban mutane da kasa baki ɗaya.