Mutum 77 sun kamu da Kanjamau a jihar Taraba

Gwamnatin jihar Taraba ta bayyana cewa mutum 77 sun kamu da cutar kanjamau a jihar.

Gwamnatin ta ce an gano wadannan mutane bayan an yi musu gwajin cutar da Wanda hukumar dakile yaduwar cutar kanjamau ta jihar (TACA) ta yi.

Hukumar TACA tare da hadin gwiwar kungiyoyin bada tallafi dake kasar nan suka shirya shirin yi wa mutane gwajin cutar da bai wa wadanda suka kamu da cutar magani kyauta domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Shugaban hukumar TACA Garba Danjuma wanda ya sanar da haka ranar Lahadi ya ce shirin wayar da kan mutane game da cutar, yi wa mutane gwajin kyauta da bai wa wadanda suka kamu da cutar magani kyauta na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin dakile yaduwar cutar nan da shekarar 2030.

Danjuma ya ce daga cikin mutum 36,396 dake dauke da kwayoyin cutar kuma ke karbar magani a jihar mutum 20,200 sun samu raguwar yawan kwayoyin cutara cikin jikin su.

“Burin gwamnati shine kawar da kanjamau gaba daya a jihar.

“NACA ta yi wa mutum 2,156 gwajin cutar inda daga ciki mutum 77 na dauke da cutar a kananan hukumomi 16 a jihar.

“Mun Kuma yi wa yara 359 masu shekaru 0-14 gwajin cutar.

“Daga cikin mutum 77 dake dauke da cutar mutum 76 sun fara karbar magani nan take.

Bayan haka shugaban kungiya mai zaman kan sa ‘Reaching Impact and Saturation Epidemic Control (RISE Nigeria) Joseph Chiegil ya jinjina wa gwamnatin jihar Taraba kan daukar matakai domin dakile yaduwar kanjamau nan da shekarar 2030 da take yi.