Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo

A ranar Juma’a ce Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo su ka tabbatar da ceto wasu ƙananan yara 50 da aka kulle a cikin wani coci da garin Ondo.
An ruwaito cewa an ceto yaran daga cikin wani kurkukun da aka gina a ƙarƙashin ƙasa a cikin cocin wanda ke unguwar Valentino.
Ana zargin dai dukkan yaran ƙananan sato su aka yi aka kulle a ɗakin da ke ƙarƙashin ƙasa a cikin cocin, domin a sayar da su.
‘Yan Sanda sun damƙe faston cocin, wanda har zuwa yau ba a bayyana sunan sa ba. Su kuma yaran su na hannun ‘yan sanda ana kula da su.
Sannan kuma ‘yan sanda sun kama wasu mambobin da ke ibada a kullum a cikin cocin.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa yaran dukkan su na can ofishin CID na Jihar Ondo, kuma ana ci gaba da bincike.
Ta ce da an kammala bincike ne a ofishin CID za a miƙa waɗanda ake zargin da safarar yara ƙanana, domin a hukunta su.