Minista Sadiya ta jajanta wa ‘yan kasuwar Guru da gobara ta yi wa ɓarna

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana jaje ga ‘yan kasuwar da gobara ta lashe wa dukiya a Babbar Kasuwar garin Guru a Jihar Yobe.

Gobarar ta yi sanadiyyar ƙonewar sama da shaguna 300 tare tare da lalata dukiyar miliyoyin naira a ƙarshen makon da ya gabata.

Hajiya Sadiya ta bayyana asarar da cewa babba ce, yayin da kuma ta umarci Hukumar Kai Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta gudanar da binciken gani-da-ido kan bala’in domin a san yawan asarar da aka yi.

Ta ce, “Ina miƙa saƙon jaje ga gwamnatin Jihar Yobe da waɗanda bala’in gobarar ya shafa wanda ya ragargaza Babbar Kasuwar Nguru. An yi asarar dukiya ta miliyoyin naira sanadiyyar wannan gobara a yayin da kuma aka rasa sana’ar yi.

“Wannan ba kawai asarar tattalin arziki kaɗai ba ce ga jihar har ga ƙasa baki ɗaya. Mu na fatan za a binciko abin da ya jawo wannan wuta don a magance faruwar irin hakan a nan gaba.

“Jami’an Hukumar Kai Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) wadda ke ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Agaji sun riga sun ziyarci kasuwar domin su gano girman asarar, da fatan gwamnati za ta shiga ciki ta taimaki waɗanda abin ya shafa.”

Duk da yake ba a kai ga bayyana wa duniya musabbabin gobarar ba, amma rahotanni sun ce shaguna da sito-sito masu yawan gaske sun ƙone ƙurmus a lokacin bala’in.

Tawagar jami’an NEMA daga ofishin yankin Arewa-maso-gabas na hukumar sun ziyarci kasuwar domin su ceto abin da za a samu daga gobarar tare da haɗin gwiwar Hukumar Kai Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe.