MATSALOLIN KIWON LAFIYA A MATAKIN FARKO: Jihohin Zamfara, Sokoto da wasu 16 ke kan gaba

Sakamakon bincike da aka gudanar a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan ya nuna cewa jihar Zamfara da wasu jihohin 17 na daga cikin jihohin dake fama da matsaloli samar da kiwon lafiya.

Sauran jihohin dake fama da matsaloli a cibiyoyin kiwon lafiyar su sun hada da Sokoto, Taraba, Kebbi, Katsina, Borno, Yobe, Kogi, Jigawa, Rivers, Gombe, Cross River, Edo, Bayelsa, Akwa-Ibom, Filato, Imo da Kaduna.

Kungiyar National Advocates for Health, Nigeria Health Watch, Public and Private Development Centre (PPDC) da sauran kungiyoyin suka gudanar da binciken mai taken ‘Matsstin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a Najeriya’.

Abin da binciken ya nuna

Binciken ya nuna yadda cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a Najeriya ke fama da matsalolin rashin amfani da kudirin tsarin BHCPF, rashin amfani da dokan ‘National Health Act’ da ‘National Health Policy’.

Sakamakon binciken ya nuno yadda samun lafiya mai nagarta a asibitoci gwamnati ke da matukar wahala ga mutane a kasar nan.

Binciken ya kuma gano hanyoyin da za su taimaka wajen inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan da suka hada da karfafa amfani da kudirin tsarin BHCPF da tsaro hanyoyin da za su taimaka wajen samar da lafiya ta gari wa mutane a cibiyoyin lafiya
Cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasar nan na fama da wadannan matsaloli saboda rashin samun shugabanin ta gari da rugujewsr fannin kiwon lafiya a kasar nan.

Shugaban kungiyar ‘Health Watch’ Vivianne Ihekweazu ta ce binciken da aka gudanar ya taimaka wajen nuna matalsalolin da cibiyoyin kiwon lafiyar kasar nan ke fama da su da hanyoyin shawo kansu.

Vivianne ta ce sakamakon binciken zai taimaka wajen jawo hankalin masu ruwa da tsaki a fannin lafiya wajen ganin sun kafa kudirorin da za su taimaka wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan.

Jihohin da suka fi Samar da lafiya ta gari a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan.

Babban birnin tarayya Abuja da jihar Enugu, Anambra ne jihohin da suka inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan.
Sauran jihohin da suka yi kokari wajen samar wa mutane lafiya ta gari a cibiyoyin lafiyar sun hada da Ekiti, Delta, Abia, Lagos, Nassarawa, Adamawa, Kwara, Benue, Ebonyi, Oyo, Bauchi, Ogun, Ondo, Kano, Niger da Osun.

Shugaban kwamitin kiwon lafiya ta majalisar dattawa Ibrahim Oloriegbe ya ce kamata ya yi a tabbatar cewa kudirin tsarin BHCPF na aiki domin inganta rayuwar mutane a kasar nan.

Oloriegbe ya ce BHCPF ta Yi aiki yadda ya kamata a Abuja saboda hadin kan majalisan dokoki ta ƙasa da dattawa.

Ya ce hakan da aka yi aka samu nasara a Abuja ya kamata a yi a duk fadin kasar nan.

” Muna kuma kira ga mutane da su taimaka wajen karkato da gwamnatocin jihohin su domin ware kudaden da za a bukata domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan.

“Hakkin gwamnatocin jihar ne su tabbatar cewa akwai kauan aiki da ma’aikata isassun a cibiyoyin lafiyar

Rashin ingantaccen shugabancin

Shugaban kungiyar ‘ONE Campaign Nigeria Stanley Achonu ya ce rashin samun shugabanin na gari na daga cikin matsalolin dake gurguntar da fannin kiwon lafiya a Najeriya.

Achonu ya inganta fannin kiwon lafiya a kasar nan ya rataya a kafadun sassan gwamnati.

Ya ce hada hannun da sassan gwamnati suka yi a shekarun baya ya taimaka wajen hana yaduwar cutar Shan inna, korona da Ebola.

“Hada hannu da sassan gwamnati suka yi ya nuna cewa gwamnati za ta iya yakan kowace irin cuta da inganta fannin lafiyar kasan.

Gwamnati ta keto cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin Samar wa mutane lafiya ta gari musamman ga mazauna karkara.

Sai dai bincike ya nuna cewa cibiyoyin kiwon lafiya Kashi 20% ne kadai ke aiki a kasar nan.

Rashin ma’aikata, rashin kayan aiki, rashin ingantacen during aiki na daga cikin matsalolin dake gurguntar da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasar nan.

Shugaban kunyiyar Improved leadership National Advocates for Health Group Muhammad Usman ya yi kira ga shugabanin gwamnati da su yi shugabanci na gari domin inganta fannin lafiyar kasar nan.

Usman ya ce hakkin gwamnati tarayya ce ta tabbtar an saki kudin hukumar BHCPF sannan hakkin gwamnatin jihohi ne su tabbatar an kashe wadannan kudade yadda suka kamata.