Mata ta roki kotu ta raba aurenta da mijinta saboda matsalar tabuwar hankali da ya samu

Kotun Magajin Garin Kaduna ta saurari karar da wata mata mai suna Lubabatu Ibrahim mai shekara 25 mazauniyar Rigasa, da ta nemi kotu ta raba aurenta da mijin ta Habibu Ibrahim saboda matsalar ƙwaƙwalwa da ya same shi, wato tabuwar hankali.

A zaman da kotun ta yi a wannan mako Lubabatu ta bayyana wa kotun cewa ɗan su daya da Habibu.

Ta ce Habibu na fama da matsalar farfadiya sannan idan dare yayi haka kawaibsai ya rika kwarara man ihu a gida.

“Idan abun ya motsa sai ya yi kacakaca da duk wani abu da ya kai ga

Bayan haka Lubabatu ta kara bada hujjar cewa Habibu baya iya gamsar da ita a gado inda da ya fara sai ya sauka.

“Habibu minti biyu kacal ya ke yi idan muka gamu a gado. Na bashi shawarar ya je ya ga likita amma ya ki.

Habibu dai bai musanta duka abin da Lubabatu ta fadi akan sa ba amma ya ce yana ganin likitan mahaukata sannan yana shan maganin gargajiya domin samun kuzari wajen jima’i.

Mijin ya roki kotu kada ta raba auren sa domin har yanzu yana son matarsa.

Alkalin kotun Malam Salisu Abubakar-Tureta ya umurci ma’auratan da su gabatar da magabatan su a zaman da kotun za ta yi ranar 21 ga Satumba.