Masarautar Katsina ta dakatar da Hakimin Kankara, saboda zargin mu’amala da ’yan bindiga

Masarautar Katsina ta dakatar da Hakimin Kankara, Abubakar Yusuf, bisa zargin sa da mu’amala da ’yan bindiga.

Kakakin Masarautar Katsina Iro Bindawa ne ya sanar da haka a ranar Asabar, biyo bayan korafe-korafen da mazauna Kankara da rahoton tsaro da aka bayan su ka tabbatar da hannun sa wajen mu’amala da masu garkuwa da mutane.

Bindawa ya ce an dakatar da basaraken domin taimaka wa kokarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi wajen ganin ta kakkabe masu garkuwa da hare-haren ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Masarautar Katsina tun da farko ta kafa kwamiti domin binciken gano gaskiyar ko basaraken na Kankara na mu’amala da ‘yan bindiga ko ba ya yi.

Masarautar Katsina ta ce za ta mika rahoton binciken ta ga gwamnatin jiha domin daukar matakina gaba a kan sa.

A Kankara ne dai a cikin watan Disamba, 2020 aka sace daliban sakandaren kwana sama da 300.

Irin wannan hadin-baki da masu garkuwa da ‘yan bindiga da ake kama masu rike da sarautun gargajiya na yi, ya na maida hannun agogo baya wajen shawo kan mahara a jihohin Zamfara da Katsina.

A ranar Juma’a ce kuma wasu ‘yan bindiga su ka bindige Auwalun Daudawa, gogarman da ya shirya yadda aka yigarkuwa da daliban Kankara.

An bindige Dudawa a cikin dajin Zamfara, bayan ya tayar da tubar sa.