Kuncin rayuwa bai hana jami’an kwastan fasa kantinan ’yan kasuwa su kwace tirelolin shinkafa ba

Jami’an Kwastan sun kutsa kasuwar Oja Oba da ke Ibadan da safiyar Asabar su ka kwace motoci cike da shinkafar da su ka yi zargin ta sumogal ce.

Kwastan din sun rika fasa kantina da suto-suto su na kwashe shinkafar da su ke zargin ta sumogal ce.

Kutsawa cikin kasuwar da jami’an kwastan su ka yi, ya faru ne wata daya bayan sun kutsa kasuwar Bodija, ta Ibadan sun kwashi shinkafar da su k ace ta asa-kwauri ce.

Kakakin Jami’an Kwastan na Shiyyar A, Theophilus Duniya, ya tabbatar da kwastan din sun fasa kasuwar, kuma sun kwashi shinkafar d ake zargin ta fasa-kwaurin ce.

“A yanzu ba zan iya kiyasta adadin ko buhun shinkafa nawa ba ne akwa kwaso daga cikin kaduwar. Abin da a kan yi, idan an kwaso kaya, za a gwada kayan a tantance, sannan a gano ko guda nawa ne.

“Maganar nan da na ke yi da kai, ban san wani abu da zan iya kadda maka ba dangane da wannan lamari. Amma dai abin da kaai zan iya ce maka a yanzu, shi ne tabbas, jami’an mu sun kai farmaki cikin kasuwar, kuma sun kwaso shinkafar fasa-kwauri.’’

Ya kara da cewa kwastan su na bin umarnin doka ce, wadda ta bas u dama shiga ko kutsawa kowace kasuwa ko ma’ajiyar abu, su kwashe shi, matsawar kayan fasa-kwauri ne.” Inji Duniya