Man fetur ɗin ƙasar nan na Najeriya ne, ba na Neja-Delta ba – Raddin Obasanjo ga Clark

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya maida wa dattijon Neja-Delta Edwin Clark kakkausan raddin cewa arzikin fetur ɗin da ƙasar nan ke da shi, na Najeriya ne, ba na Neja-Delta ba.

Cikin wasiƙar da Obasanjo ya aika wa Clark a ranar Talata, kuma ya raba wa manema labarai a Abeakuta, Obasanjo ya ce ƙarya Edwin Clark ke yi da ya ce wai shi Obasanjo ɗin ba ya ƙaunar yankin Neja-Delta.

“Kowa ya san ni a ƙasar nan, na daɗe ina kishin zamantakewar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya dunƙulalliyar. Babu ruwa na da fifita shiyya ko yanki.”

Kamfanin Dillacin Labarai ya ruwaito Edwin Clark na cewa Obasanjo ya na jin haushin yankin Neja-Delta.

Clark ya yi furucin a wurin ne a wurin taron ɗabbaƙa zaman lafiya, wanda Global Peace Foundation and Vision Africa ta shirya, kwanan nan a Abuja.

Zarge-zargen da Clark ya yi wa Obasanjo na cikin wata wasiƙar da ya aika wa tsohon shugaban na Najeriya.

A cikin raddin da Obasanjo ya yi wa Clark, ya ce masa ba daidai ba ne, Clark ko wani ɗan Neja Delta ya riƙa cewa arzikin man fetur ɗin ƙasar nan na yankin Neja Delta ne.

A kan haka Obasanjo ya ce mai Najeriya ce ke da duk wani albarkatun ƙarƙashin ƙasa, ba yankin da albarkatun ƙasar su ke ne ke da haƙƙin sa ba.

A cikin wasiƙar wadda Obasanjo ya yi wa dattijo Clark kaca-kaca, ya kira shi mai magana ya na sakin-baki, kuma bagidajen da bai waje da duniya ba.”

Obasanjo ya ce bai kamata dattijo kamar Clark ya na zantuka irin na mashaya ba.