MAJALISAR DINKIN DUNIYA: Rashin isassun maganin Korona zai iya kawo nakasu a farfadowar tattalin arzikin kasashen

Majalisar dinkin duniya UN ta bayyana cewa rashin samun isassun maganin rigakafin Korona zai iya kawo nakasu a farfadowar tattalin arzikin kasashen duniya.

Kididdigar tattalin arzikin kasashe da UN ta fitar a wannan mako ya nuna cewa an samu ci gaba a bunklasar tattalin arzikin duniya sai dai rashin isassun maganin rigakafin korona ka iya as a samu koma bayan tattalin arziki a kasashe masu tasowa.

Sakamakon binciken WESP ya nuna rashin samun daidaituwar tattalin arzikin duniya na tashi sama a ma’aunin sikelin gwaji daga kashi 3.6% a shekarar 2020 zuwa 5.4% a shekarar 2021.

“Rashin samun isassun maganin rigakafin cutar ka iya hassasa rashin samun daidaituwa tattalin arzikin kasashen duniya.

WESP ta fara gudanar da bincike a akan haka tun lokacin da korona ta bayyana a duniya.

Binciken ya maida hankali wajen yin nazari akan cutar da yadda za ta jijjiga tattalin arzikin duniya sannan da yadda gwamnatin kasashen duniya za su tunkari abin don shawo kan matsalolin da tattalin arzikin kasashe za su fada.

Zuwa yanzu tattalin arzikin kasashen Chana da Amurka sun fara farfadowar sai dai hakan ba shine ke aukuwa a kasashen dake yankin Asia ta Kudu, Kudu da Saharan Afrika, Latin America da Caribbean ba.

Tattalin kasashen duniya da dama za su fara farfadowa ne a shekarun 2022 zuwa 2023.

Kasashen dake sarrafa kaya su ne za su fara samun ci gaba a tattalin arzikin su amma kasashen da ci gaban tattalin arzikin su ya dogara da kudaden da ake samu a yawon bude ido farfadowar tattalin arzikin su ba zai taso ba saboda har yanzu mutane basu fita yawo domin gudun barkewar cutar.