KATSINA: ‘Yan sanda sun kama wasu mutum hudu da dabobbin sata 208 a Kankara

A jihar Katsina rundunar ‘yan sandan ta kama wasu mutum hudu da ta zarge su da satar dabobbi a jihar.

Kakakin rundunar Gambo Isah ya sanar da haka a wani takarda da ya raba wa manema labarai ranar Talata a garin Katsina.

Isah ya ce an kama wadannan mutane da dabobbi 208 a Kankara bayan wasu mazauna wurin sun tona musu asiri ta hanyar sanar da jami’an tsaro a boye.

Ya ce an kama Isiya Halliru, Nasiru Bature, Bello Hamza da Hassan Iliyasu ranar 10 ga Mayu.

“Wadannan mutane na tafiya da shanu 170, tumaki 38 wanda hakan ya sa muka zarge su da satar dabobbin.

Isah ya ce wadanda aka kama din sun shaida wa ‘yan sanda cewa masu dabobbin na can cikin dajin Rugu, su kiwo kawai suke musu.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike akai kafin ainihin masu dabbobin su bayyana.

Idan ba a manta ba a watan Afrilu PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan sanda suka kashe wasu mahara uku kuma ta kwato dabobbi 330 a jihar Katsina.

‘Yan sandan sun yi arangama da maharan a Mararabar-Gurbi.

An kwato babban bindiga Ak47 guda daya, shannu 160, tumaki 170 da babura biyu daga hannun maharan.

Bayan haka rundunar tare da hadin guiwar kungiyar ‘yan banga sun kama Ibrahim Ma’aruf, mai shekaru 40, a kauyen Runka dake karamar hukumar Safana.
Ma’aruf ya shahara wajen yin garkuwa da mutane, siyar da makamai da sace-sacen dabobbi.

‘Yan sanda sun kama Ma’aruf a dalilin bayanan sirri da wasu suka sanar da yan sandan bayan ganinsa da suka yi da dabobbi 40 a Dutsen-Ma kusa da karamar hukumar Safana.

‘Yan sanda sun dade suna neman Ma’aruf ruwa a jallo domin akwai ranar da Ma’aruf ya gudu ya bara harsashin babban bindiga na Ak47 guda 96, tsabar kudi Naira 780,000 a shingen tsaron ‘yansanda dake hanyar Dutsinma zuwa Safana da ya ga ‘yan sanda za su ritsa da shi.