Majalisar Dattawa za ta rage wa shugaban ƙasa ƙarfin yin gabagaɗin tsige shugaban EFCC

Ƙudirin neman kafa dokar taƙaita wa shugaban ƙasa yin gabagaɗin tsige shugaban EFCC ya tsallake siraɗin karatu na biyu a zauren majalisa a ranar Talata.
Ƙudirin dai na so a yi wa doka kwaskwarima, ta yadda za ta hana shugaban ƙasa yin gabagaɗin tsige shugaban EFCC ba tare da amincewar Majalisar Dattawa ba.
“Ta haka ne kawai za a iya bai wa wa’adin shugabancin EFCC garanti,” inji ƙudirin neman a yi wa dokar garambawul.
Sanata kuma Balaliyar Majalisa na Marasa Rinjaye, Chukwuka Utazi ne ya gabatar da ƙudirin.
Utazi ya ce matsawar ana so a kare shekarun wa’adin kowane shugaban EFCC, to dole sai an yi wa dokar da ta kafa Hukumar kwaskwarima, ta yadda sai da amincewar Majalisar Dattawa sannan shugaban ƙasa zai iya tsige shugaban EFCC.
Majalisar Dattawa za ta rage wa shugaban ƙasa ƙarfin yin gabagaɗin tsige shugaban EFCC.
Ƙudirin neman kafa dokar taƙaita wa shugaban ƙasa yin gabagaɗin tsige shugaban EFCC ya tsallake siraɗin karatu na biyu a zauren majalisa a ranar Talata.
Ƙudirin dai na so a yi wa doka kwaskwarima, ta yadda za ta hana shugaban ƙasa yin gabagaɗin tsige shugaban EFCC ba tare da amincewar Majalisar Dattawa ba.
“Ta haka ne kawai za a iya bai wa wa’adin shugabancin EFCC garanti,” inji ƙudirin neman a yi wa dokar garambawul.
Sanata kuma Balaliyar Majalisa na Marasa Rinjaye, Chukwuka Utazi ne ya gabatar da ƙudirin.
Utazi ya ce matsawar ana so a kare shekarun wa’adin kowane shugaban EFCC, to dole sai an yi wa dokar da ta kafa Hukumar kwaskwarima, ta yadda sai da amincewar Majalisar Dattawa sannan shugaban ƙasa zai iya tsige shugaban EFCC.
Haka nan kuma wannan ƙudiri zai tabbatar ganin an yi wa dokar EFCC kwaskwarima, ta yadda sai daga cikin ma’aikatan EFCC ɗin kaɗai za a iya naɗa wa hukumar EFCC shugaba.