Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa a ciwo bashin dala miliyan 700 domin kashe su ga aikin ruwan sha

Kwana ɗaya bayan Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa a ciwo bashin dala miliyan 200 domin a lakaɗa wa sauro dukan tsiya da kuɗin, a ranar Laraba kuma ta ƙi amincewa a ciwo bashin dala miliyan 700 domin a yi aikin samar da ruwan da kuɗaɗen.

Kwamitin Lura da Tulin Basussuka na Majalisar Dattawa ne ya ƙi amincewa a ciwo bashin, a lokacin da Babban Sakatare ta Ma’aikatar Harkokin Ruwa ta Tarayya, Esther Wilson ta gabatar da bayanin ciwo bashin, wanda ke cikin Kasafin 2022 na Shugaba Muhammadu Buhari.

An yi niyyar kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗe ne a Shirin Samar da Ruwan Sha Tsaftatacce a Birane da Karkara (SURWASH).

Shugaban Kwamitin Lura da Basussuka na Majalisar Dattawa, Clifford Ordia, ya ce ba zai yiwu su amince a ciwo bashin ba, domin sauran basussukan da Mai’aikatar Ruwan Sha ta ciwo, ba su ga aikin da aka yi da kuɗaɗen ba.

Daga nan sun umarci Ma’aikatar Ruwa ta je ta bi diddigin kuɗaɗen da ta ciwo bashi a baya, tare da kawo hujjojin ayyukan da aka yi da kuɗaɗen, domin kwamitin ya tantance.

“Me aka yi da lamunin AfDB na dala miliyan 450 da aka ce za a kashe wajen inganta madatsar wura ta Gurara? Ina wani lamunin na dala miliyan 6 na aikin ruwa kuma?

“Ta yaya za a ciwo bashi a ciki har a rubuta za a ware wa kowace jiha dala miliyan shida domin bayar da horo ga ma’aikatan harkokin ruwa? Su jihohin ba za su iya horas da ma’aikatan na su ba ne?”

Har aka tashi daga taron dai Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Ruwa ta Tarayya, ba ta iya cewa komai ba.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Majalisar Dattawa ta ƙi yarda a ciwo bashin dala miliyan 200 domin sayo gidan sauro ga jihohi 12.

Majalisar Dattawa ta yi fatali da roƙon da Ma’aikatar Harkokin Lafiya ta Tarayya ta yi, inda ta nemi amincewa ta ciwo bashin dala miliyan 200 daga waje, domin sayo gidan sauron da za a raba a jihohi 13 da za a kori zazzaɓin maleriya.

Kwamitin Lafiya na Majalisar Dattawa ne ya ƙi amincewa da buƙatar, a lokacin da Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya, Mahmuda Mamman ya yi masu bayanin cewa kuɗaɗen da za a sayo gidajen sauron ma ramto su za a yi.

Sanata Ibrahim Olomiegba, ɗan APC daga Jihar Kwara ya ce wannan Sagegeduwa ce kuwa dabarar rashin dabara.

Ya ce ai a cikin Kasafin 2022, an ware Naira miliyan 450 domin yaƙi da zazzaɓin cizon sauro. “Don me kuma za a nemi iznin mu a ce wai a ciwo bashin dala miliyan 200 a sayo gidajen sauro?

Tun da farko dai Mahmuda ya ce idan an sayo gidan sauron, za a raba su ne a jihohi 13 daga jihohi 36 na ƙasar nan.

Ya ce za a raba su ne a cikin ƙananan hukumomi 208.

A ƙarshe dai Sanata Abba Moro da sauran mambobin kwamitin su ka ce ba za a ciwo bashin ba. Waccan Naira miliyan 450 ta cikin kasafin 2022 ta wadatar.