Mun kammala titunan sama da naira biliyan N88.4 da Sule Lamido ya yi watsi dasu – Badaru

Gwamnatin Gwamna Muhammad Badaru na Jihar Jigawa tace ta kammala dukkanin aikin tituna da ta gada a mulkin Tsohon Gwamna Sule Lamido daga shekarar 2015 wanda kudinsu ya kai har fiye da biliyan N88.4

Kwamishinan Ayuka da Sufuri na Jihar Jigawa, Aminu Rola, ya shaidawa manema labarai, a birmin Dutse, ranar Laraba, cewa titunan da suka gada sun wuce tsahun kilomita 716 wadda gwamnatin Sule Lamido ta biya yan kwangila fiye da biliyan N32.5 kacal.

Aminu Rola yace gwamna Badaru ya sami ragi daga wajen Yan kwangila har na biliyan N7.5 billion a cikin N88.4

Bayan ragi da aka samu, da kuma biliyan N32 da aka biya a gwannatin baya, kudin titunan sun kai biliyan N48.3 a inda gwamnatin Gwamna Muhammad Badaru ta biya biliyan N45.4 kuma ta adana miliyan N39 bayan kammala dukkanin ayukan titunan, inji Kwamishina, Aminu Rola.

Kwamishinan yace gwamnatin Jigawa ta sami nasarar hakan ne duk da rashin kudin shiga mai gwabi da kuma matsin tattalin arziki saboda tsantseni da kaffa-kaffa da gwamna Badaru yakeyi wajen kashe kudin al’ummu a inda ya dace.

Gwamnatin mu a shekarar 2015 ta gaji kudi miliyan N16 kacal a asusun Jihar Jigawa amma saboda tattali da dukiyan al’umma irin na mai girma Gwamna, yau Jihar Jigawa tana daya daga cikin Jahohin da ke iya ayukan cigaban al’umma da kuma biyan albashi a kan lokaci, inji Aminu Rola.