MAJALISA A 2021: Yadda Majalisar Tarayya ta yi zama sau 70, maimakon sau 181 wanda doka ta gindaya masu

Dokar Najeriya a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki ya gindaya wa Majalisar Tarayya da ta Dattawa sharuɗɗan cewa “Majalisa za ta zauna aƙalla sau 181 a cikin shekara ɗaya.” Haka Sashe na 63 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya gindaya.

Amma sai ga shi Majalisar Tarayya ta zauna sau 70 kaɗai a cikin 2021, wato ko rabin adadin zaman da doka ta gindaya masu ba su yi ba.

Dama PREMIUM TIMES ta buga cewa a watanni ukun ƙarshen shekarar 2021, wato Oktoba, Nuwamba da Disamba, ta zauna sau 14 kacal.

Doka ta amince Majalisar Tarayya ta zauna daga Litinin zuwa Juma’a.

Wannan jarida ta buga labarin yadda Majalisar Dattawa ta zauna sau 66 kaɗai a cikin 2021.

Amma kuma bayan da Premium Times ta buga labarin, sai Kakakin Yaɗa Labaran Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa, wato Ezrel Tabiowo ya shaida wa jaridar cewa “ai zaman kwamiti ma ana lissafa shi a matsayin zaman majalisa.”

Amma wani lauya mai zaman kan sa mai suna Jiti Ogunye, ya ce Tabiowo ya yi kuskure, bai faɗi daidai ba.

“A ina Kakakin Yaɗa Labaran Sanata Ahmad Lawan ya samo hujjar cewa zaman kwamiti na cikin lissafin zaman majalisa? Domin babu wannan bayanin a cikin dokar Najeriya. Ka je ka duba ma’anar zaman majalisa a sashe na 318 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya. Babu inda ya ce zaman kwamiti na cikin adadin zaman majalisa.”

Kakakin Majalisar Dattawa Sanata Ajibola Bashiru, ya bayyana dalilin cutar korona ne ya kawo ƙarancin zaman majalisun a 2021. Ya kuma yafa mayafin wasu dalilan bayan na korona, ya lulluɓe majalisar da su.

Wani lauya mai suna Kelechukwu Eni-Otu, ya yi raga-raga da hujjojin da Majalisar Dattawa ta bayar.

“Zaman Majalisa ba akushin abinci kala-kala ba ne, da ‘yan Majalisa za su ce sai wanda su ka zaɓa za su ci. Abin da doka ta ce, shi ne wajibin abin da ya dace a yi.” Inji shi.

Haka kuma ya ce rashin kunya ce da ‘yan majalisa su ka kafa hujja da korona. Domin ai duk da ba su zaman, sun ci gaba da karɓar kuɗaɗen alawus-alawus na su na zaman duk da ba su yi ba.

Cikin 2022: Yadda Majalisar Dattawa Ta Yi Zama Sau 66, Maimakon Sau 181 Da Doka Ta Gindaya:

Majalisar Dattawa, inda can ne ake kafa dokokin da ke cikin Kundin Mulkin Najeriya, ta kasance ita ce a sahun gaba wajen karya dokokin Najeriya a shekarar 2021.

Tsarin Mulkin Najeriya ya gindaya cewa wajibin Majalisar Dattawa ne ta yi zama na aƙalla sau 181 a kowace shekara, wato zaman kwana 181 a cikin kwanaki 365.

Maimakon haka, dattawan ba su dubi darajar dokokin da su ke kafawa ba, kuma ba su daratta gemun su ba wajen bin ƙa’ida. Sai su ka yi zama sau 66 kacal a cikin kwanaki 365 na shekarar 2021.

Sannan kuma dattawan sun karya ƙa’idar da Majalisa ta gindiya, inda “Umarni na 13(2) ya ce su rika zama a ranakun Talata, Laraba da Alhamis a kowane mako.”

Majalisar Dattawa ta karya wannan umarni, inda a cikin 2021 ta riƙa zama a ranakun Talata da Laraba kawai.

Hakan na nufin Majalisar Dattawa ta yi zaman watanni biyu da kwanaki shida kaɗai, maimakon zaman yawan kwanakin watanni shida cur.

PREMIUM TIMES ta binciko cewa Majalisar Dattawa ta tafi hutu har sau takwas a cikin 2021. Kuma hutun kan kama daga mako ɗaya har zuwa makonni huɗu.

Tsakanin 34 Ga Fabrairu, zuwa 22 Ga Disamba, Majalisa ta je hutu sau takwas.

Hutun kan kasance ko dai na tafiya zaman makokin wani ɗan majalisa da ya mutu, hutun Sallah ko na Kirsimeti, ko kuma hutun tafiya duba-garin ayyuka a matsayin su na kwamitin ɓangarori daban-daban.

Hutun farko da su ka fara tafiya a cikin 2021, shi ne hutun da aka bayar domin Sanatocin APC su je su yi sabunta rajista tare da tantance ‘yan jam’iyya.

A farkon 2021 dai kamata ya yi a ce sun koma aiki a ranar 23 Ga Janairu, 2021. Amma sai aka ƙara hutun zuwa 9 Ga Fabrairu, domin ‘yan APC su samu damar zuwa sabunta rajistar jam’iyya. Daga nan kuma sai da su ka ƙara tafiya wani hutun har sau bakwai a cikin 2021.

‘Yan Najeriya da dama na ganin cewa kamata ya yi a daina kashe biliyoyin kuɗaɗe wajen tafiyar da majalisa. Su na ganin a rage yawan su, kuma kowa ya zauna a jihar sa, sai ranar zaman majalisa ya je ya halarta.