ƘADDAMAR DA DALAR SHINKAFA: RIFAN ta ce shinkafa za ta fi kowane kayan abinci arha a Najeriya har sai an riƙa fita dashi waje

Ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Ƙasa (RIFAN), ta ce shirye-shirye sun kammala inda Buhari zai ƙaddamar Dalar Samfarerar Shinkafa a Abuja, ranar Talata.

Shugaban Kwamitin Tara Tulin Dalar Shinkafa na RIFAN ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa (NAN) cewa tara wanann irin Dalar Shinkafa mai yawa haka ya nuna cewa Najeriya za ta iya ciyar da kan ta.

A ranar Talata ne Shuagaba Buhari ya ƙaddamar da Dalar Shinkafa, a taron da manyan jami’an gwamnati su ka halarta, har da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

An tara tulin dalar shinkafa Samfarera mai tarin yawa a daidai Shoprite na Lugbe da ke kan hanyar zuwa Babban Filin Jirgin Sama na Abuja.

Buhunan Samfarerar dai ba a caje su ba, kuma an tara har buhu miliyan ɗaya cur, waɗanda aka ɗauko daga jihohi da daban-daban na ƙasar nan, a ƙarƙashin shirin ‘Anchor Borrowers’ na CBN.

Mu’azu ya ce za zaran an kammala ƙaddamar da Dalar Shinkafa ɗin, za a raba ta ga masu sarrafa shinkafa daban-daban a ƙarƙashin RIFAN.

“RIFAN ce tare da haɗin guiwar Ƙungiyar Masu Sarrafa Shinkafa ta Najeriya, za su cashe shinkafar sannan su sayar da ita a farashi mai sauƙi ga jama’a.” Inji shi.

“Za mu shiga gaba domin mu ga mun tabbatar da farashin shinkafar da ake nomawa a gida ya faɗi ƙasa warwas, da zaran an fara tunkuɗa wannan shinkafar a cikin kasuwanni.

“Dama kuma yarjejeniyar da muka yi da Ƙungiyar Masu Cashe Shinkafa cewa za su sayar da ita a farashi mai rahusa ga ‘yan Najeriya.

“Duk da dai ba za mu iya magana a kan farashin da za a yanke ba, duk dai da cewa a yanzu farashin kayan abinci ya cilla sama sosai.

“Amma dai ina tabbatar maku cewa shinkafa za ta fi kowane irin abinci arha a ƙasar nan, sakamakon wannan gagarimin shiri.” Inji shi.

Ya ce “shirin ‘Anchor Borrowers’ shaida ce cewa Gwamnatin Tarayya ta magance matsalar kayan abinci.”