Mai Mala Buni ta rushe shugabacin APC a Zamfara, ya naɗa Matawalle shugaba

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban jam’iyar APC na ƙasa a matakin riƙon ƙwarya Mai Mala Buni, ya buƙaci ɗaukacin membobin jam’iyyar a Jihar Zamfara da su baiwa Gwamna Matawalle goyon baya a matsayin sa na sabon shugaban su wajen ganin sun yi aiki tare domin samar wa da jihar ci gaba.

Da yake jawabi bayan an danƙa masa tutar jam’iyar APC, Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya ce a matsayin sa na sabon wanda aka naɗa a matsayin shugaba, zai tabbatar da yin adalci ga kowanne bangare na ƴaƴan jam’iyyar.

Ya kuma yi ƙira ga dukkannin ƴanƴan jam’iyar da su bashi hadin kai domin gina jam’iyar APC da jihar ke so.

Yayin jawabin sa wajen taron, tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari yace ya amince da matsayin da jam’iyyar ta ƙasa ta ɗauka kuma a shirye yake ya baiwa Gwamna Matawalle goyan bayan da yake buƙata.

Yari ya buƙaci Gwamnan da yayi taka tsan-tsan da waɗanda ya bayyana a matsayin masu hana ruwa gudu wajen haɗa kan jama’a.

Bikin karbar Gwamna Matawalle ya samu halartar Gwamnonin Jihohin Borno da Katsina da Ogun da Filato da Kano da Kogi da Kaduna da Jigawa da Niger da kuma Kebbi tare da Sakataren Gwamnatin tarayya da ministoci da ƴan Majalisun Dattawa da na wakilai.