KURUNKUS: Bayan jan rai da karyata komawa APC da ya rika yi, Matawalle ya tsunduma APCn tare da dubban ƴan Zamfara

Da yammacin Talata ne gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya tsunduma jam’iyyar APC bayan jan rai da ya rika yi wa jam’iyyar watanni da yawa a baya.

An yi gagarimar taron yi masa wankar dauɗar PDP a filin wasa da ke Gusau kuma taron ya samu halartar jigajigan ƴan jam’iyyar APC da suka hada da gwamnoni da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Kusan dungurugun ɗin ƴan PDP kaf ɗin su suka marawa Matawalle baya zuwa cikin APC.

Sai dai kuma mataimakin gwamnan, Mahdi Aliyu Gusau bai bi gwamnan ba, ya ce shi yana nan a jam’iyyar sa ta PDP. Tare da shi akwai wani ɗan majalisan jiha Kabiru Yahaya, basu bi gwamnan ba.

Dalilin da ya sa mataimakin gwamnan jihar Mahdi ya ki bin gwamna Matawalle shine ya ce Kotu ta baiwa PDP ne kujerar gwamna ba APC ba, saboda haka shi yana nan a jam’iyyar PDP.

Rigerigen komawa APC

Tsohon sakataren Jam’iyyar APGA na kasa Sani Shinkafi ya koma jam’iyyar APC bayan shekaru 19 da yayi a jam’iyyar APGA.

Shinkafi ya bayyana cewa da kansa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bukaci ya koma jam’iyyar APC tare da shi, a yau Talata.

” Na koma APC tare da duka ƴan jam’iyyar APGA kaf ɗin su dake ke kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.

Haka kuma a majalisar Tarayya ranar Talata, kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya sanar a zauren majalisar cewa ƴan majalisa Lego Idagbo, dake wakiltar Beckwara/Obudu/Obanliku da Michael Etaba dake wakiltar Obubra/ Etung, jihar Koross Ribas duk sun fice daga PDP sun koma jam’iyyar APC.

Har yanzu dai daga jihar Zamfara, Sanata Hassan Gusau ya canja sheka zuwa APC daga PDP.

Sanata Hassan Gusau na daga cikin wadanda suka samu kujerar tsinci kujerar sanata daga sama gasassa domin a dalilin hukuncin kotun ƙoli da ya soke zabukan APC gana ɗaya ya bai wa PDP ya sa suke bisa kujeru yanzu.