Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, John Hayab ya bayyana cewa mahara sun saki dalibai 10 cikin dalibai 31 da suka ragd ke tsare a hannun su.
Idan ba a manta ba a watan Yuli, mahara sun sace dalibai 131 daga makarantar Bethel dake Kaduna. A hankali bayan wasu lokutta, sun rika sako daliban akai akai har zuwa ranar Asabar da suka sako mutum 10.
Hayab yace akwai sauran dalibai 21 dake tsare a hannun ‘yan bindiga.