KWALARA: Mutum 100 sun mutu a jihar Neja

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Neja, Muhammad Makusidi ya bayyana cewa cutar Kwalara ta yi ajalin mutum 100 daga watan Afrilu zuwa yanzu a jihar.

Makusidi ya fadi haka da yake zantawa da manema labarai a taron inganta amfani da dabarun bada tazarar haihuwa da Kungiya mai zaman kanta ‘Pathfinder International’ ta shirya a garin Minna.

Ya ce rashin tsaftace muhalli da yin bahaya a waje na daga cikin dalilan da ya sa cutar ta yi mummunar barkewa da yin ajalin ƴan jihar.

Makusidi ya ce gwamnati ta fara aikin wayar da kan mutane hanyoyin guje wa kamuwa da cutar domin samun kariya sannan ta zuba magungunan cutar a asibitoci sune mafita.

Kwamishinan ya kuma yabawa haɗa hannu da gwamnati ta yi da kungiyar ‘Pathfinder International’ domin inganta amfani da dabarun bada tazaran haihuwa a jihar.

“Inganta amfani da dabarun bada tazaran iyali na daga cikin dabarun da gwamnati ta dauka domin samar wa kowa da kowa lafiya ta gari a jihar.

Ya ce matsaloli da suka shafi al’adun gargajiya, adini, rashin isassun dabarun bada tazaran haihuwa, rashin isassun kudade, rashin tsaro na daga cikin matsalolin da ke hana mutane amfani da dabarun bada tazaran haihuwa a jihar.

Kwalara a Najeriya

A wannan mako ne hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Ƙasa (NCDC), ta bayyana cewa mutum 46 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar amai da gudawa a kasar nan.

Rahotan ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar ta kashe an gano su ne daga jihohi 8 a kasar nan.

Jihohin sun hada da Borno-13, Sokoto-12, Katsina-8, Bauchi-6, Niger-3, Kaduna-2, Adamawa-1 da Kano 1.
Hukumar ta ce bisa ga rahotan da ta samu daga ranar 30 ga Agusta zuwa 5 ga Satumba ya nuna cewa a jihohi 25 da Abuja tun da aka shiga shekaran 2021.

Mutum 1,677 sun kamu da cutar a cikin mako daya a jihohi 12 inda hakan ya kawo jimlar yawan mutanen da suka kamu da cutar zuwa mutum 69,925 a kasar nan.

Jihohin da mutum 1,677 suka kamu sun hada da Bauchi-566, Katsina-282, Sokoto-258, Yobe-183, Borno-179, Niger-94, Kaduna-66, Adamawa-34, Gombe-8, Kano-4, Kebbi-2 da Nasarawa-1.

Abubuwa 10 dake haddasa barkewar cutar a kasar nan

1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.

2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.

3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.

4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.

5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.

6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.

7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.

8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.

9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.

10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.