Kungiyar Fulani Da Ke Aikin Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Koya Wa Mata 200 Sana’o’in Hannu A Nasarawa

Kungiyar Fulani ta Walidra da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Najeriya ta koya wa mata fulani 200 sana’o’i hannu a Rugan Julie da ke karamar hukumar Karu ta Jihar Nasarawa domin taimaka masu su samu dogaro da kansu daga mawuyacin halin da yan bindiga suka jefa yawancin su a ciki.