Kungiya ta yi korafi kan sahihancin takardun karatun ɗan takarar gwamnan Bauchi na APC, ta roki INEC ta soke takarar sa

Akwai yiwuwar hukumar zaɓe (INEC) ta cire sunan dan takarar gwamnan APC na jihar Bauchi, Abubakar Sadique Baba, idan har ta amince da bukatar da aka gabatar mata game da hakan.
Abubakar Sadique Baba ya riƙe muƙamin babban hafsan sojan sama kafin ritayarsa da kuma shiga siyasa.
Ya zama ɗan takarar jam’iyyar APC a Bauchi ne bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani wanda aka gabatar a cikin watan Mayu.
Bukatar neman cire sunan Abubakar Sadique a matsayin ɗan takara na cikin wata takarda da wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Accountability and Democratic Project (ADEP) ta rubutawa shugaban hukumar INEC.
Kungiyar ta yi koken cewa dan takarar bai gabatar da cikakkun takardunsa ba ga hukumar zaben, kamar yadda doka ta tanada.
A cewar kungiyar, Abubakar bai sanya wasu muhimman takardunsa waɗanda za su tabbatar da bayanan da ya cike a form din INEC mai suna EC 9 ba.
Babban darektan kungiyar Ahmed Muhammad wanda shine ya saka wa takardar korafin kungiyar hannu ya ƙara da cewa wasu daga cikin takardun da Sadique ya mika wa hukumar zaɓen akwai alamar tambaya akan su matuka dake ƙalubalantar cancantar sa ya yi takarar gwamnan jihar Bauchi.
Da muka yi kyakkyawar dubi da nazarin takardun da ya mika wa hukumar zaɓe, ɗan takaran ya ce an haife shi ne a garin Azare, sanna kuma yace ya yi makarantar firamaren sa a St Paul kuma ya gama a shekarar 1973 da dai sauransu. Ɗan takaran bai mika kwararan takardun da zasu nuna sannan su tabbatar cewa lallai abubuwan da ya rubuta gaskiya ne.
Duk wanda ya bi waɗannan takardu dalla-dalla zai kokwanton tabbacin karatun sa na firamare da sakandare domin babu sahihan bayanai da zasu tabbatar maka cewa gaskiya ne lamurran karatun na sa.