Ku kare kanku daga ’Yan Bindiga amma kar ku karya doka~ Gwamnan Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ƙirayi mazauna jihar da su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga amma su tabbatar ba su karya doka ba, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Yankin Arewa-maso-Yamma da jihar ke ciki na ɗaya daga cikin yankunan da ‘yan ta’adda suka fi addabar al’umma.
“Mutane kada su ɗauki doka a hannunsu, amma ya kamata su ɗauki matakan doka yadda ya kamata don kare al’ummominsu yayin da wasu gungun ‘yan ta’adda suka afka musu,” in jiwata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Ibrahim Magaji Dosara ya fitar a ranar Laraba.
“Gwamnatin jihar ta amince da mutanen da ke kusa da yankunan ‘yan ta’addan da ke cikin jihar da su fito ƙwansu da ƙwarkwatansu domin kare kansu a duk lokacin da ‘yan ta’addan suka far wa al’ummarsu.”
Sanarwar ta kuma sanar da cewa ‘yan sanda sun cafke masu aikata laifuka 35 “wadanda suka hada da galibin masu satar mutane, masu ba da bayanai da wadanda ke taimaka wa ‘yan bindiga a jihar.” “An yi masu tambayoyi kuma sun amsa laifuffukansu daban-daban kuma tuni aka tura su Abuja don ci gaba da bincike kafin a hukunta su.”
Hakanan, gwamnatin jihar ta ce ta ɗage haramcin da aka sanya kan harkokin kasuwanci a kasuwanni huɗu a jihar. “Matakin ya biyo bayan kiraye-kiraye da dama daga wasu ‘yan ƙasa da ke damuwa a ciki da wajen jihar, don ɗage haramcin tare da bai wa talaka damar samun bukatunsa na yau da kullun a cikin watan Ramadana.
“Kasuwannin da abin ya shafa su ne Magami, Wanke, Ɗansadau da Dauran,” in ji sanarwar.
“An hana kasuwannin huɗu yin kowane irin hada-hada a makon da ya gabata bayan hare-hare da kisan mutane da basu ji ba basu gani ba a cikin al’ummomin da abin ya shafa.”