‘Ku bazama cikin daji ku ceto ɗaliban Islamiyya 200 da aka sace’ -Gargaɗin Buhari ga jami’an tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargaɗi jami’an tsaron Najeriya cewa su bazama cikin daji kuma su tabbatar ba su dawo hannu biyu ba, sai tare da ɗaliban Islamiyya 200 da ‘yan bindiga su ka sace a Tegina, cikin Jihar Neja.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, wato Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa Buhari ya karbi rahoton sace yaran kuma cikin fushi ya umarci dukkan bangarorin jami’an tsaron da nauyin ceto yaran ke wuyan su, su gaggauta ceto su daga hannun ‘yan bindigar.

Ya kuma nuna fushin sa dangane da yadda ake sakaci har ‘yan bindiga ke yawan kwasar ɗalibai masu tarin yawa, har ɗaruruwa su na nausawa daji da su.

Sannan kuma Buhari ya umarci hukumomin da abin ya shafa su gaggauta kai wa iyayen yaran da aka sace aka yi garkuwa da su, tallafin duk da su ke buƙata.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda mahara su ka kutsa garin Tegina, cikin Ƙaramar Hukumar Rafi, su ka yi awon-gaba da ɗaliban Islamiyya kimanin 200.

Gwamnatin Jihar Neja ta ce maharan sun sako yara ƙanana 11, saboda sun yi ƙanƙanta da yawa, kuma ba su iya tafiya a cikin daji.

Gidan Radiyon Sashen Hausa na BBC ya yi hira da Shugaban Makarantar, wanda ya shaida cewa ya yi magana da ‘yan bindigar, inda ya roƙe su cewa aka su azabtar da yaran, kuma kada su wulaƙanta su.

Ya ce maharan sun yi masa alƙawarin ba za su doke su ko gajiyar da su ko wulaƙanta su ba.

Sai ya ƙara da cewa ya tambayi maharan su faɗa masa yawan ɗaliban da su ka sace, sun ce ba za su faɗi yawan su ba.

PREMIUM TIMES ta kuma buga labarin da Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello ya ce halin da jihar ke ciki, ba shi da bambanci da zamanin yaƙuƙuwan ‘ƙatilan maƙatulan’.