Kotu ta tsare magidanci da ya yi lalata da yarinya ta dubura a kurkukun kirikiri

Kotun majistare dake Ikeja jihar Legas ta yanke wa wani mai gidan buredi mai shekara 36 Samuel Emmanuel hukuncin dauri a kurkukun Kirikiri bayan an kama shi da laifin yi wa ‘yar karamar yarinyar fyade ta bubura.
Alkalin kotun Mrs B.O. Osunsanmi ta yi watsi ta rokon sassaucin da Emmanuel ya nema sannan ta yanke hukuncin cewa Emmanuel zai yi zaman kurkukun har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka.
Ta ce za a ci gaba da shari’ar ranar 25 ga Janairu.
Dan sandan da ya shigar da karar Raji Akeem ya ce Emmanuel dake zama a Ileejo dake Lekki ya aikata wannan ta’asa ne ranar 25 ga Nuwambar 2022 a Ile-Ojo dake Ibeju a Lekki.
Akeem ya ce a wannan rana Emmanuel ya kira wata yarinya karama dake tallan ganda da ta kawo masa gandar sai ya damke ta da karfin tsiya ya ciccibeta ya kutsa da ita cikin daki har ya yi lalata da ita ta dubura
Ya ce makwabta sun ji ihun yarinyar amma kafin su kawo mata dauki Emmanuel ya riga ya yi abin da zai yi da ita.