Ina rokon kotu ta raba aure na da Yusuf kada wata rana ya kashe ni da duka – Ramatu a Kotu

Wata mata mahaifiyar ‘ya’ya biyar Ramat Abideen ta roki kotun gargajiya dake Mapo a Ibadan da ta raba auren ta na shekara 18 da mijinta Yusuf saboda yawan lakada mata dukan tsiya da yake yi.
Ramat ta ce tun da ta tare gidan Yusuf shekaru 18 da suka gabata take cin dukan tsiya kan abin da bai taka kara ya karya ba.
“ Yusuf abokin wa na ne kuma duk da cewa wa na bai amince ba kuma Yusuf bai biya kudin sadakin aure na ba na tare a gidan sa.
“ Bayan na tare gidan sa Yusuf ya karbi naira 83,000 da nake tarawa domin na siya fili, tun daga lokacin ya rika wulakanta ni tare da ci mini mutunci.
“ Yusuf ya ci gaba da duka na duk da cewa ya karo mata sannan na amince na bi shi wurin aikinsa a Igboora.
“ Mun haifi yaya biyar tare inda daya daga cikinsu ya zo da nakasa a jikinsa amma Yusuf ya ki kula da yaron.
Ramat ta ce tana bukatar kotu ta taba auren kada wata rana Yusuf ya kashe ta da duka.
A zaman da kotun ta yi Yusuf bai zo kotun ba.
A dalilin haka alkalin kotun Mrs S.M. Akintayo ta raba auren.
Akintayo ta gargadi Yusuf kada ya sake cin zarafin Ramat sannan ta bai wa Ramat ikon kula da yaran da suka haifa.
Alkalin ta ce Yusuf na da ikon ganin ‘ya’yan sa a duk lokacin da yake so sannan Ramat da Yusuf za su hada hannu wajen biyan kudin kula da makaranta da bukatan ‘ya’yan su.