Kotu ta bada belin ‘yan buyagin da su ka kai hari gidan Babbar Mai Shari’a Mary Odili

Babbar Kotun Tarayya ta bada belin mutum 11 daga cikin mutum 15 ɗin da aka gurfanar bisa tuhumar su da harin da aka kai gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙolin Najeriya.
An caje su da laifin fojare ɗin sammacin kotu, shiga gidan wani ba da iznin sa ba, tsoratarwa da tatsar kuɗaɗe.
An kai wa gidan Mary Odili farmakin neman yin bincike a gidan ta bisa umarnin wani alƙalin ƙaramar kotu na bogi a Abuja.
Mai Shari’a Nkeonye Maha ta Kotun Tarayya ta bayar da belin su a kan naira miliyan 5 kowanen su. Sannan kuma kowa zai ajiye fasfo ɗin sa na fita waje a kotun.
Haka nan kuma kowanen su mutum biyu masu mutunci ne zai su tsaya masa a kotun. Kuma mutanen biyu su kasance ɗaya mazaunin Abuja ne wanda ya mallaki gida ko fili a Abuja.
Mutum na biyu kuma zai kasance ya na aiki ne a Abuja, kuma ya mallaki takardar biyan haraji ta shakara uku. Kuma za su ajiye takardar fili ko gidan da kuma takardar haraji a kotu.
Mutane uku da ba a bada belin su ba, sun haɗa da ASP Mohammed Yahaya, Abdullahi Adamu da kuma Abdullahi Usman.
Mai Shari’a ta ce za a ci gaba da tsare su a kurkukun Kuje saboda babu wanda ya nemi belin su, har zuwa ranakun 17 da 18 Ga Janairu, ranar da za a fara shari’ar gar-da-gar.
Akwai kuma mutane bakwai da ake nema ruwa a jallo, bayan sun cika wandon su da iska.
Kotu ta ce su ma waɗanda aka bayar da belin a ci gaba da tsare su a kurkuku, har sai wanda ya cika sharaɗin beli sannan a sake shi.