KORONA: Mutum 209 sun kamu da ranar Laraba

Alkaluman sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba ya nuna cewa an samu karin mutum 209 da suka kamu da cutar sannan mutum daya ya mutu a Najeriya.

Hukumar ta ce gano haka ne daga jihohi 11 da Abuja.

Zuwa yanzu mutum 212,359 ne suka kamu, an sallami 204,010 sannan har yanzu mutum 5,688 na dauke da cutar.

Mutum 2,890 ne suka mutu a dalilin kamuwa da cutar.

Idan ba a manta ba daga Litini zuwa Talata mutum 189 be suka kamu da cutar sannan mutum biyu sun mutu.

Yaduwar cutar

Legas – 77863, Abuja-23,319, Rivers-12,728, Kaduna-10,031, Filato-9,799, Oyo-8,758, Edo-6,594, Ogun-5,374, Kano-4,360, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,571, Kwara-3,930, Delta-4,096, Osun-3,006, Enugu-2,768, Nasarawa-2,517, Gombe-2,691, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-2,017, Imo-2,053, Bauchi-1,736, Ekiti-1,775, Benue-1,863, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,250, Bayelsa-1,243, Niger-1,056, Sokoto-796, Jigawa-604, Yobe-501, Cross-Rivers-645, Kebbi-458, Zamfara-302, da Kogi-5.

Bayan haka mutanen jihar Legas sun yi kira ga gwamnati da ta Kara yawan asibitocin gwamnati da ake yin allurar rigakafin korona a jihar.

Mutanen sun yi wannan kira ne saboda cikan da mutane ke yi a asibitocin gwamnatin da ake yin allurar rigakafin kyauta a jihar.

Da dama sun ce a dalilin haka ya sa basa samun yin allurar rigakafin cutar.

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ta fara hirar da jami’an lafiya 400 domin Kara yawan ma’aikatan dake yi wa mutane allurar rigakafin.
Gwamnatin ta Kuma ce za ta hada hannu da fannin dake zaman kansu domin karaya yawan asibitocin da ake yi wa mutane allurar rigakafin kyauta.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa za ta yi wa mutum miliyan 4 allurar rigakafin korona a jihar Nan da ranar 25 ga Disemba.

Gwamnatin ta Kuma bai wa mutanen jihar zabi ko su yi rigakafin cutar a asibitin gwamnati kyauta ko Kuma su biya Naira 6,000 domin su yi a asibitin dake zaman kansu.