‘Yan bindiga sun yi wa wasu ‘yan mata fyade da basu samu abin dauka a gidan mahaifin su ba

Rundunar tsaro na Sibul Difens NSCDC reshen jihar Kwara ta bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Nuku dake karamar hukumar Kaiama ranar uku ga Nuwanba.

Kakakin rundunar Babawale Afolabi ya fadi haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar Alhamis a garin Ilorin.

Afolabi ya ce a kauyen maharan sun afka gidan wani Alhaji Hassan Yunusa inda suka sassare shi da wani dan uwansa Woru Yunusa da adduna sannan suka tafi da ‘ya’yan sa mata kanana biyu cikin daji.

Daga baya sai suka saki yaran a amma kuma sai da suka yi lalata da su wato suka yi musu fyade.

“Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa maharan sun shigo wannan kauye don su yi fashin kudaden mutane ne da ba su samu kudin ba sai suka tafi da ‘yan matan suka aikata abinda suka ga dama da su.

Afolabi ya ce likitoci na duba ‘yan matan kuma rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo maharan.