Korar sarki Sanusi daga Kano ya saba wa dokar kasa, kotu ta ce Ganduje ya biya shi naira miliyan 10

Kotu a babban birnin tarayya ta umarci gwamnatin Kano karkashin gwamna Abdullahi Ganduje ta biya tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi naira miliyan 10 kan korar sa da ta yi daga garin Kano bayan tsige shi daga sarautar Kano.

Da take yanke hukunci kan karar da Khalifa Sanusi ya shigar, alkalin kotun, Anwuli Chikere, ta ba umarci a biya shi diyyar Naira miliyan 10 da kuma wadanda ake karan da suka hada da ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) da kuma babban lauyan jihar Kano.

Sannan kuma ta umarce su da su rubuta shimfidaddiyar wasikar ban hakuri ga Sanusi a manyan jaridu guda biyu.

Chikere ta ce hukuncin da gwamnatin Kano ta ɗauka bayan tsige Sanusi cikin 2019 ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ta ce Sanusi na da ‘yancin ya ci gaba da zama a Kano, ko ya kai ziyara idan ya ga dama.

“Dokar Masarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaƙaba ta 2019 kan Sarki Muhami Sanusi, haramtacciya ce. Saboda ta kauce wa kundin dokokin Najeriya.”

A kan haka kotu ta ce Hukumar ‘Yan Sanda, SSS da Gwamnatin Jihar Kano biya Muhammadu Sanusi diyyar Naira miliyan 10, saboda sun ɗauke shi zuwa Abuja da ƙarfin tsiya, daga can suka wuce da shi jihar Nassarawa.

A ranar 12 Ga Maris, 2020 Muhammadu Sanusi ya shigar da ƙarar tauye masa haƙƙin walwala. Amma bai ɗaukaka ƙarar tsige shi da aka yi ba.