KARYEWAR DARAJAR NAIRA: Ba haukan yawo tsirara ba, har dukan mutane da kulki sai Naira riƙa yi – Kingsley Moghalu

“Matuƙar dai a kullum Najeriya za ta ci gaba da dogaro da ɗanyen man fetur, to kuwa tabbas duk wata darajar Naira sai ta zube tamkar barushin goge takalmi”.

Tsohon Mataimakin Shugaban Babban Bankin Najeriya (CBN), Kingsley Moghalu ne ya bayyana haka.

Moghalu ya bayyana a shafin sa na Facebook cewa Naira a yanzu ta na bisa siraɗi ne, wanda ceto ta sai fa idan tattalin arzikin Najeriya ya na iya samar wa kan sa kuɗaɗen dogaro da kai, tare kuma da iya jure goyayya da tsere da gasa a hada-hadar kasuwancin duniya.

“Matsawar ba mu faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga mu ka daina dogaro da ɗanyen man fetur shi kaɗai ba, to Naira za ta ci gaba da rugurgujewa ta koma tubalin toka.” Inji Moghalu.

Ya ce lamarin ya wuce hada-hadar kashu ko sayar da muƙa-muƙan tulin doya a waje. Cewa ya yi sai Najeriya ta fara fitar da kayayyakin da ke bunƙasa harkoki da fannonin injiniyanci da ƙirkire-ƙirƙire.

Bayanan Moghalu sun zo ne sanadiyyar yadda Naira ke ta yin faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa, har kwankwason ta ya fashe.

CBN dai ya ce ba zai sauya tsarin daina sayar da dala ga ‘yan canjin BDC ba.

Sannan kuma ya zargi gidan yanar gizo na abokiFX.com da ruruta tsadar dala, ta hanyar riƙa buga farashin da shaci-faɗi ne kawai.