BASHI BA YA SA GABAN KA YA FAƊI: Buhari ya bayyana yadda zai yi tsantsenin kashe dala biliyan 5 da zai sake rikitowa bashi

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kashe fiye da dala biliyan 4 wajen gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa har guda 15 a faɗin dukkan yankunan ƙasar nan shida.

A ranar Litinin ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin ya kinkimo bashin dala biliyan 4.054 da kuja fam na Ingila 710 da Dala 125, domin yin ayyukan raya ƙasa.

Wasiƙar dai ta ce za a karɓo basussukan da Bankin Duniya, French Development Agency (AFD), China Exim Bank, IFAD, Credit Suisse Group da Standard Chartered/China Export and Credit (SINOSURE).

Dalla-dallar yadda za a kashe kuɗaɗen dai ta nuna cewa Bankin Duniya (World Bank) zau ɗauki nauyin aiwatar da ayyuka har guda bakwai, ciki kuwa har da kashe dala miliyan 125 wajen bunƙasa fannin ilmi, a ƙarƙashin shirin “Better Education Services for All”, da sauran su.

Jihohin da za su ci moriyar ayyukan bunƙasa harkokin noma, sun haɗa da Kogi, Kaduna, Kano, Cross River, Enugu, Lagos.

Za a yi ayyukan a ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Noma da Inganta Rayuwar Karkara ta Ƙasa.

Premium Times ta ruwaito Sanatan APC ya koka da yawan tulin bashin da Buhari ke ciwowa, da yadda Majalisa ke gaggawar amince masa.

Sanata Ali Ndume daga Jihar Barno ya nuna matuƙar damuwa ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke giringiɗishin yawan ciwo bashi.

Ndume ya kuma nuna damuwa ganin yadda Majalisar Dattawa a koda yaushe ta ke rawar-jikin amincewa da dukkan buƙatu da dalilan ciwo bashin da Buhari ke gabatarwa a Majalisa.

Sanatan ya ce abin haushi da takaici, har yanzu babu wasu muhimman ayyukan raya ƙasa birjik a ƙasa da za a iya tinƙaho da su, waɗanda za a ce an gina su ne daga cikin maƙudan kuɗaɗen bashin da ake ciwowa.

Ndume ya yi wannan tsokaci a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, a Abuja.

Sanatan ya na magana ne dangane da bashin da Buhari ya aiko neman amincewar Majalisar Dattawa domin ya ciwo, waɗanda kuɗaɗen a yanzu za su iya kai naira tiriliyan 2.2. Kuma dama ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 33.

Yayin da PDP ke cewa bashin da Buhari zai ƙara ciwowa zai ƙara burma ‘yan Najeriya cikin ƙuncin rayuwa, APC kuwa cewa ta ke yi bashin “alheri zai zama ga ƙasar nan. Da kuma inganta rayuwar ‘yan ƙasar su kan su.

“Ni ba masanin kuɗaɗe ba ne. Amma batun gaskiya ba karɓo bashin ne matsala ba. Inda matsalar ta ke shi ne abin da za a yi da kuɗaɗen da kuma yadda za a riƙa kulawa da su.”

Ndume ya ce akwai basussukan da na tilas ne, akwai kuma waɗanda ake ciwowa haka kawai don giringiɗishi.

“Akwai ƙarancin kayayyakin inganta rayuwa a faɗin ƙasar nan. To kuma mu na jin nan a Abuja da kuma a bakin sauran jama’a cewa idan aka fitar da kuɗaɗe, sai a rasa abin da ake yi da su. Domin babu wani abin a zo a gani da za a iya shaidawa.”

Haka nan kuma Ndume ya nuna ɓacin rai ganin yadda idanun Majalisar Dattawa ke rufewa su riƙa gaggawar amincewa da dukkan buƙatun ciwo bashi da Buhari ke aika masu neman amincewar su.

Farkon watan Agusta Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya ya nuna damuwa kan tulin bashin da Najeriya ke ciwowa.

Sai dai kuma a cikin makon da ya yi ƙorafin ne, sai Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta ce tulin bashin ba mai kumbura ciki ba n.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa har yanzu bashin da Najeriya ke ciwowa bai kumbura mata cikin da zai iya fashewa ba.

Ministar ta ce har yanzu Najeriya ba ta tsallake ƙa’idar Gejin Tattalin Arzikin Cikin Gida na ba, inda ta ce har yanzu bashin bai wuce kashi 23 bisa 100 ba.

Zainab ta yi wannan bayani ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin.

Cikin makon jiya ne Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta bayyana malejin Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) ya ƙaru zuwa kashi 5.01 a watannin Afrilu, Mayu da Yuni na 2021.

Zainab ta ce ai babu wani abin damuwa, domin kuɗaɗen da ake rantowa ana yin ayyukan raya ƙasa ne da su, waɗanda su ka haɗa da aikin lantarki, titina, samar da ruwa da titinan jiragen ƙasa, waɗanda su ne ƙashin bayan inganta tattalin arziki.

“Mu na ciwo bashi a cikin yin taka-tsantsan ɗin da har yanzu ba mu wuce kashi 23 na Gejin Ma’aunin GDP ba.

“Na sha faɗa ba sau ɗaya ko sau biyu ba cewa babbar matsalar ƙasar nan ita ce ƙarancin kuɗaɗen shiga, waɗanda ƙarancin na su ke sa tilas a ke ciwo basussuka domin a yi ayyukan raya ƙasa da inganta tattalin arzikin cikin gida.”

Kwanan baya ne Majalisar Tarayya ta damu da tulin bashin da Gwamnatin Tarayya ke ciwowa, alhali hukumomi ba su zuba kuɗaɗen shiga asusun Gwamnanti.

Kwamitin Lura da Kuɗaɗen Gwamnantin Tarayya na Majalisar Tarayya ya nuna ɓacin rai ganin yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.62 domin narkawa a yi ayyukan raya ƙasa a kasafin 2021, amma kuma a gefe ɗaya hukumomin Gwamnantin Tarayya da yawa sun riƙe kuɗaɗen shiga sun ƙi zubawa a cikin Asusun Gwamnantin Tarayya domin a samu kuɗaɗen yin ayyuka.

Shugaban Kwamitin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya James Feleke ya ce, “a gaskiya ba mu jin daɗin yadda wasu hukumomin gwamnati ke riƙe kuɗaɗe ba su zubawa cikin asusun Gwamnanti, ita kuma gwamnati an bar ta fita gaganiyar ciwo basussukan da za ta yi ayyukan raya ƙasa.

“Don Allah ya zama wajibi mu tashi mu nuna kishin ƙasar mu don mu ci moriyar bunƙasar ta baki ɗayan mu.”

Feleke ya magana ne ganin yadda wasu hukumomin Gwamnantin Tarayya su ka kasa bada bayanai wasu kuma su ka ƙi zuba kuɗaɗen shigar su a Asusun Gwamnantin Tarayya tsawon lokaci.

Kwamitin dai na gayyatar Hukumomi ne ɗaya bayan ɗaya su na gabatar da bayanan kuɗaɗen shigar da su ke tarawa duk shekara, domin a ji yadda za a yi kirdadon kuɗaɗen shigar da za su tara daga shekarar 2022 zuwa 2024.

“Ɗaya daga cikin matsalar ƙasar nan ita ce rashin wadattattun kuɗaɗen shiga a aljihun gwamnatin tarayya. Dalili kenan Majalisar Tarayya ke son sanin adadin kuɗaɗen shigar da kowace hukuma ke tarawa a kowace shekara.” Inji Feleke

“Wasu ayyuka da dama da hukumomin gwamnati ke yi duk kashe maƙudan kuɗaɗe ne kawai ake yi a hanyar da ba ta cancanta ba. Kamata ya yi su daina bayar waɗannan manyan ayyuka na manyan kwangiloli, su maida hankali wajen tara wa Gwamnatin Tarayya kuɗaɗen shiga kawai.

Daga Feleke ya juya wajen Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), inda ya umarce ta cewa ta gabatar da bayanan kuɗaɗen da ta tara tun daga shekarun 2018, 2019 da 2020.