KARIN KUDIN MAKARANTA: An dakatar da karatu a jami’ar Kaduna, KASU – Inji Rajistara Manshop

Rajistarar Jami’ar Jihar Kaduna, KASU, Samuel Manshop ya sanar cewa gwamnatin ta dakatar da Karatu a jami’ar karkakakaf har sai illa-ma-shaAllahu.

Manshop bai bayyana dalilan da ya sa aka rufe makarantar ba sai dai ya ce dakatarwar bai shafi daliban dake karatun aikin likitanci ba, da masu karatu na gaba da digirin farko da wadanda ke karatu na karshen mako.

Wannan dakatarwa ya shafi dalibai da ke karatu digiri a jami’ar.

Idan ba a manta ba Daliban jami’ar jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewar su ga karin kudin makaranta da gwamnatin jihar tayi.

Daliban sun ce wannan kari zai sa wasu da dama su ajiye karatun saboda ba za su iya biyan kudin makaranta ba.

Sai dai kuma a cikin makon jiya, wasu jami’an gwamnatin jihar Kaduna sun gana da Daliban, wanda a zaman suka shaida musu cewa gwamnatin El-Rufai kaifi daya ce, ba zata rage kudin makarantar ba.

Gwamnati ta yi kira ga daliban su nemi koda bashin yin karatu domin su yi karatu ko kuma tallafin karatu daga gwamnati.