KARAMBANI KO KARAMBANA: Ahmed Isah ya dakatar da tarawa ASUU naira biliyan 18, bayan an tara naira miliyan 12

Fitaccen mai gabatar da shirin Hembelembe na ga dan radiyon Human Rights FM dake Abuja, Ahmed Isah, ya dakatar da tarawa kungiyar malaman jami’o’i naira biliyan 18.
Hakan ya biyo bayan nesanta kansu da wannan asusu ne da kungiyar malaman ta yi a ranar Asabar.
Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar nan ASUU, Emmanuel Osodeke ya ce babu hannun ƙungiyar a asusun da Ahmed Isah ya buɗe wai jama’a su tara taro-sisi har naira biliyan 18 domin a baiwa ASUU don su janye yajin aikin da suke yi.
Kafin ya sanar da dakatar da asusun wanda ya buɗe a bankunan GTB da na Jaiz, Isah ya ce an tara naira miliyan 12 zuwa yanzu. Sannan kuma har gwamnan jihar Akwa-Ibom Emmanuel Udom ya bada gudunmawar naira miliyan 50.
Idan ba a manta ba Ahmed Isa, mai gabatar da shirin Hembelembe a radiyon Human Right dake Abuja ya buɗe asusu inda yayi kira ga ƴan Najeriya su saka kuɗi domin tara naira biliyan 18 a biya malaman makaranta don su janye yajin aikin da suke yi.
ASUU ta ce Isah ya gaggauta cire sunan ASUU a jikin wannan asusu.
Kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya sun ja daga watannin hudu kenan sasantawa bai yiwu ba a tsakani.
Daliban makarantun gwamnati kaf suna gida saboda yajin aikin.
Ra’ayoyin jama’a
Da yawa daga cikin mutane sun soki wannnan tara kuɗi da Ahmed Isah ya ƙirkiro, suna masu cewa wannan ba hurumi ne na sa ba.
” Niyyar da yake da shi yayi kyau amma kuma naira biliyan 18 ake magana. Idan aka ce ƴan Najeriya ne za su rika tara kuɗi suna baiwa malaman don su janye ya jin aiki ai koma baya kenan.
” Yau idan aka tara wannnan kuɗi aka baiwa malaman, gobe kuma idan hakan ya sake aukuwa yaya za ayi. Da abinci za a ji ko kuwa da tara wa malaman jami’o’i kudin albashi.
” Manyan Najeriya duk sun tura ƴaƴan su kasashen waje da makarantu masu zaman kansu a faɗin kasar nan. Dama dai ƴaƴan talakawa ne a jami’oin. Ta ina za a tara naira biliyan 18. Shi mai ba’a ya ke yi ko.
” Abinda ya fi da cewa shine ya ci gaba da amfani da kafar sa wajen yin kira ga gwamnati su gaggauta kawo karshen yajin aikin domin ɗalibai su koma makaranta. Hakan shine kawai gudunmawar da zai iya bada wa.