‘Kar ku zabi duk ɗan takaran shugaban ƙasa da shekarunsa ya wuce 60’-IBB

Tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Babaginda ya ƙi ya goyi bayan manyan ƴan siyasa biyu dake kan gaba wurin neman kujerar shugabancin Najeriya a zaben 2023 dake tafe, wato Asiwaju Bola Tinubu, da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

A wata hira da yayi da gidan talabijin na ARISE a ranar Juma’a, IBB ya ce ya kamata shugaban Najeriya na gaba kar ya wuce shekaru 60.

Duk da cewa Tinubu da Atiku ba su fito fili sun bayyana sha’awar su a zaben 2023 ba, amma akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa dukkan su biyu suna da sha’awar takarar.

IBB ya ce yana da aƙalla mutane uku a zuciyar sa da zai so ɗaya daga cikin su ya zama shugaban Najeriya a shekarar 2023 kuma dukkan su babu wanda shekarunsa ya wuce sittin.

Atiku, mai shekaru 75, zai cika 77 a shekarar 2023, yayin da Tinubu, wanda ya cika shekaru 68 a watan Maris, zai cika shekaru 70 a zabe mai zuwa.

Ya ce, “Na fara hango nagartaccen shugaban Najeriya. Wato, wanda ke yawo a duk faɗin ƙasar nan kuma yana da abokai kusan a duk inda ya ziyarta. Yana da aƙalla mutum ɗaya da zai iya yin magana da shi a ko ina.

“Wannan mutum ne, wanda yake da ƙwarewa a fannin tattalin arziki kuma ɗan siyasa ne nagari, wanda ya kamata ya iya magana da ƴan Najeriya da sauransu. Na ga mutum kusan ko uku da irin waɗannan siffofin masu shekaru sittin.”