KANO: Rashin iya biyan kuɗin jarabawar NECO ya sa Ɗanladi ya babbake kansa

Wani saurayi mazaunin garin Garo, Karamar Hukumar Kabo, jihar Kano dildila wa kansa fetur ya cinna wuta saboda ya kasa biyan kuɗin jarabawar NECO.

Wasu da abin ya faru a Idon su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito sun bayyana cewa sau uku Ɗanladi na rubutu jarabawar amma baya ci.

” Ranar da Ɗanladi zai aikata abin da yayi, sai da ya dawo wurin koyon aikin sa na kanikanci. A hanyar dawowa gida ya siyo fetur a gora ya shiga da shi ɗaki a gidan su.

Mutane sun ce sun ji ya na ihu ne a ɗaki, ya na cewa ” Jama’a a ceceni, a kawo min ɗauki. ” Daga na sai makwabta suka shiga suka kashe wutan aka wuce da shi asibiti.

Sai dai kuma rai yayi halin sa ne kwana biyu bayan an kwantar da shi a asibiti.

Wani makwabcin marigayi Ɗanladi ya shaida cewa marigayin ya taba tara rabin kuɗin amma ya kashe su saboda ya kasa samun sauran.