Buhari ya naɗa Farfesa Attahiru Jega sabon muƙami

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Attahiru Jega, tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Jos.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, wanda ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, ya ce Shugaba Buhari ya kuma amince da naɗin tare da sake tura wasu shugabannin Jami’o’in gwamnatin tarayya 42.

Wasu daga cikin shuwagabannin sun haɗa da;

Jami’ar Benin- HRM Farfesa James Ortese Iorzua Ayatse.

Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, Bauchi- Oba Rufus Adeyemo Adejugbe Aladesanmi III.

Jami’ar Ahmaɗu Bello Zaria, jihar Kaduna- HM Obi Ofala Nnaemeka Alfred Achebe.

Jami’ar Alex Ekwueme daje Ndufu-Alike, jihar Ebonyi- HRM Oba Aremu Gbadebo.

Jami’ar Bayero Kano-HM, Oba Ewuare 11,
Basaraken Benin.

Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse, jihar Jigawa- HRM Sarki W S Joshua Igbugburu X, Con, Ibenanawei na masarautar Bomo.

Jami’ar gwamnatin tarayya daje Gashua- HRM Farfesa Joseph Chike Edozien. CFR, Sarkin Asaba.

Jami’ar tarayya Lokoja, jihar Kogi- HRH Alhaji (Dr.) Mohammadu Abali Ibn Mohammed Idris, CON, Sarkin Fika.

Jami’ar tarayya Dutsin-ma, jihar Katsina- Sarki Dandeson Douglas Jaja Jeki, Amanyanabo na masarautar Opobo.

Jami’ar Michael Okpara, Umuduke- HRH Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, Sarkin Gombe.