Kabiru Gombe ya yi ikirarin maka tsohon Kwamishinan jihar Kano a kotu

Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya ce zai maka tsohon Kwamishinan aiyyuka na jihar Kano Engr. Muaz Magaji (Win-Win) bisa abin da ya ƙira da mata masa suna.

Shaihin Malamin ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda yake ƙaryata wani rubutu da ɗan siyasan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Kabiru Gombe ya “gargaɗi shugaban jam’iyyar APC na ƙasa mai riƙon ƙwarya Mai Mala Buni da cewa muddin Sanata Rabi’un Musa Kwankwaso ya dawo APC suma za su fice daga cikin ta”.

Kabiru Gombe ya wallafa cewa, “Assalamu’alaikum

Ni Muhammad Kabir Haruna Gombe, nayi Allah wadai da karya da wani bawan Allah daga jihar Kano mai suna Muaz Magaji ya kirkira kuma ya jingina ta gareni. Kamar yadda yace nayi waya da Gwamna Mai Mala Buni akan maganar siyasa, ni tunda nake ban taba waya da Mai Mala Buni ba ko akan menene, domin wannan ba shine a gaban mu ba.

Mu ba ‘yan siyasar jam’iyya bane, bamu da jam’iyya a siyasa, illa kawai muce da jama’a su zabi wanda mukewa zaton mutumin kirki ne, in zabe yazo mu cewa jama’a su zabeshi, ballatana har nayi barazanar fita daga wata jam’iyya zuwa wata jam’iyya.

Wannan karya da ya kwantara min mai hade da cin mutunci mafi kololuwa a rayuwa, sam ba’a yita ba, bamu da alaka da duk wani mai mulki da ya wuce alaka ta addini.

Dan haka mun baiwa wannan mutum mai suna Muazu Magaji awanni goma sha biyu (12hours) da ya fito ya janye maganarsa ko mu kai kara zuwa kotu, Dan Baza mu saka ido a wannan karya da ya mana tare da cin mutunci ya tafi a banza ba matukar bai fito ya karyata kansa ba.

Jama’a su kwantar da hankalin su, Tuni muka fara daukan mataki na turawa lauyoyin mu domin subi mana hakkin mu a kotu karkashin “Sashin Doka da Hukunci” na (Defamation of character) ‘Bata suna ko Zubar da mutunci’ “Sashi na 391 na Kundin Tsarin Laifuka da Hukunci (Penal Code).

Kuma muna da tabbacin kotu zata mana adalci wajen hukunta shi akan laifin da yayi matukar ya gagara kawo hujjojin sa akan wannan kage da cin mutunci ta yadda zai zama darasi ga ‘yan baya masu hali irin nashi.

Ma’assalam”.

Tun da farko ga abin da Muazu Magaji ya wallafa a shafinsa da ya janyo Sheikh Kabir Gombe ya mayar da martani.

Ya wallafa a shain sa da cewa Su Kabir Gombe sun ce “Muddin Kuka Shigo Da Kwankwaso Jam iyyar APC, To Mukuma Zamu Barta Sakon , Kabiru Gombe , Ga, Mai Mala buni Shugaban jam iyyar APC,

Tunidai Aka Nadi Wata Waya da Akai Tsakanin Kabiru Gombe Da Shugaban jam iyyar APC Mai Mala Buni,

Hakan Yabiyo bayan Wasu Bayanan Sirri Dasuke Bayyana , Wanda Ake Ganin Tsohon Gwamnan Na jihar Kano Dr , Rabiu Musa Kwakwaso Yana Daf Da Komawa jam iyyar ta APC,

Idan Masu Karatu Zasu iya tunawa Kusan Watanni2 Da suka Wuce Shugabanna APC Ya mikawa Kwakwaso Tayin Komawa jam iyyar APC duba Dacewar Uwa baya jindadin Wasu Abubuwa Dasuke Faruwa A jam iyyar tasa Ta PDP,

Wannan tasa Kwakwaso ya nemi Abashi , Minista Guda 1 Sannan Akarbe jam iyyar APC daga Gurin Ganduje Abashi Hadi da Sakataren Gwamnatin tarayya Dama Wasu Mukamai Saidai Wannan bukata tasa Tayiwa Shugabanni na APC Tsauri,

Saidai Da Alama Yanzu Sun Yarda Da Wannan bukata tasa Wanda izuwa yanzu Ansauke Minista 1 sabo Nanono Sannan Ansauke Bashir Garba lado Wanda Za a cigaba da Sauke Wasu Domin Sharemai Hanyar Komawa jam iyyar APC”.

Engr. Muaz Magaji dai ma’abocin amfani da kafafen sada zumunta ne musamman Facebook wanda bai tsoron janyo magana ta ko ina. Katobarar magana a kafafe sada zumunta ya yi sanadiyyar rasa kujerar sa ta Kwamishina a shekarar 2020 bisa murnar rasuwan Malam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.